1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rumsfeld ya fara wata ziyarar ba zata a Iraki

April 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0a

sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld ya sauka a birnin Bagadaza a wata ziyara ta ba zata da ake gani wani goyon baya ga sabuwar gwamnatin Iraqi. Majiyoyin ma´aikatar tsaron Amirka ta Pentagon sun ce Rumsfeld zai gana da sabon FM Iraqi Jawad al-Maliki da kuma manyan kwandojin Amirka a Iraqi. Wannan ziyarar ta zo ne a cikin wani mawuyacin hali musamman bayan sukar lamirin sakataren da wasu tsofaffin hafsoshin sojin Amirka suka yi dangane da rawar da ya taka a yakin Iraqi. janar janar din su 6 sun yi kira ga Rumsfeld da yayi murabus saboda rashin iya jagoranci da kuma kurakuran da ya tabka. Shugaba Bush ya yi watsi da wannan kira.