1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rwanda ta fara karbar 'yan cirani daga Libya

Zulaiha Abubakar
September 27, 2019

Wasu 'yan cirani na kasashen Afirka da a baya suke zaune a kasar Libiya sun isa kasar ta Ruwanda bayan da hukumomin kasar sun amince da karbar su.

https://p.dw.com/p/3QMzX
Erste Flüchtlinge aus libyschen Lagern in Ruanda angekommen
Hoto: AFP/C. Ndegeya

Yawan mutanen da suka isa Ruwanda din dai ya kai 66 kuma daga cikinsu akwai mata da yara kanana , aikin kwashe 'yan ciranin daga Libiya ya biyo bayan wani roko da shugaba Paul Kagame ya yi tun a shekara ta 2017, inda ya bukaci kasar sa ta samarwa 'yan ciranin da suka fito daga kasashen Afirka mutsuguni.

A farkon wannan wata na Satumba ne Ruwanda ta rattaba hannu a yarjejeniyar hadin gwuiwa tsakaninta da  kungiyar tarayyar Afirka watau AU da kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya domin karbar masu neman mafakar da ke ragaita a Libiya.