1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sa-in-sa tsakanin Amurkawa da masu adawa gyara dokar mallakar makamai

December 21, 2012

Masu ra'ayin kyale dokar mallakar bindaga a Amurkar sun yi kira ga mahukuntan kasar da su sanya masu gadi dauke da makamai a makarantun kasar don kare dalibai.

https://p.dw.com/p/177n8
Hoto: AFP/Getty Images

Kungiyar ta National Rifle Association dai ta ce wannan mataki zai taimakawa kasar wajen ganin an kare rayukan Amurkawa a makarantu da sauran wurare.

Wannan kiran dai na kunshe ne cikin taron manema labarai da kungiyar ta yi, inda mataimakin shugabanta Wayne LaPierre ce kungiyar za ta taimakawa makarantu da horo dangane da yadda za su kare kansu.  

Amurkawa a birnin Washington dai sun gudanar da zanga-zanga ta nuna rashin amincewarsu da wannan mataki.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman