1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saadi Gaddafi ya shiga hannu

March 6, 2014

Jamhuriyar Nijar ta mika daya daga cikin 'ya'yan marigayi tsohon shugaban kasar Libiya Muammar Gaddafi, ga mahukunatan Libiyan domin a yi masa shari'a a kasarsa.

https://p.dw.com/p/1BKxj
Hoto: Reuters

Majalisar zartaswar kasar Libiyan a karkashin jagorancin Firaminista Ali Zaidan ce ta tabbatar da mika Saadi Gaddafin inda ta ce a yanzu haka yana gidan kaso a Libiyan bayan da ya iso daga Jamhuriyar Nijar din. Saadi, dai ya tsere ne zuwa Jamhuriyar Nijar tun bayan da aka kifar da gwamnatin babansa ta mulkin kama karya a juyin-juya halin da ya samu goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO a shakara ta 2011.

Saadi Gaddafi, baya daga cikin wadanda kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ke nema ruwa a jallo, sai dai mahukuntan kasar ta Libiya na son tuhumar Saadi da laifin almubazzaranci da kuma yin amfani da makami wajen firgita 'yan wasa a yayin da yake shugabantar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Libiyan. Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasar dai na neman a mika mata daya daga cikin 'ya'yan marigayi Gaddafin wato Saif al-Islam bisa zarginsa da aikata laifukan yaki, sai dai har kawo yanzu yana tsare a hannu tsagerun Libiyan masu dauke da makamai da suka cafke shi bayan kifar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman