1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabanni a kan batun bakin haure a nahiyar Turai

Küstner Kai MNA
June 22, 2018

Akwai sabanin ra'ayi tsakanin kasashen Turai dangane da matakin da ya fi dacewa a dauka na tinkarar matsalar 'yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa a kasashen EU.

https://p.dw.com/p/306od
Rettungsschiff Seefuchs
Hoto: picture-alliance/dpa/sea-eye.org

Batun da ake kai ruwa rana kai shi ne ko ya dace a bude sansanonin karbar 'yan gudun hijira a wasu kasashe da ba na EU ba, inda za a duba bukatunsu na neman mafaka. Wannan batu dai yana a jadawalin taron kolin da EU za ta yi a mako mai zuwa. A nan Jamus ma ana tabka mahawara kan batu mai sarkakiya.

Tankiya a game da bude sansanonin 'yan gudun hijira a wasu kasaShe da ke wajen kungiyar tarayyar Turai

Saatari Jordanien Flüchtlingslager Flüchtling Krieg Zaatari
Hoto: picture-alliance/dpa

Ana iya cewa shawarar bude sansanonin 'yan gudun hijirar a wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai, EU, yunkuri ne na dinke babbar barakar da ta taso tsakanin 'yan ra'ayin mazan jiya da masu sassauci a cikin kungiyar ta EU dangane da matsalar 'yan gudun hijira, wato hana duk dan gudun hijirar da aka ceto a tekun Bahar Rum damar shiga wanta kasa ta kungiyar. Maimakon haka a mayar da su wasu sansanin karbar 'yan gudun hijira a wasu kasashe da ba na EU ba. Shawarar da a fakaice shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ba ta nuna adawa da ita ba.

Ta ce: "Dole ne mu rage yawan bakin haure da ke shigo mana, amma a lokaci guda mu ba da dama ta shigowa ta halastattun hanyoyi ga masu koyon sana'a ko karatun jami'a da dai makamantansu."

Wani daftarin farko na sanarwar bayan taron da EU ke shirin gudanarwa a mako mai zuwa da ya shiga hannun ofishin gidan talabijin Jamus na ARD da ke birnin Brussels na cewa akwai bukatar a gaggauta bambamtawa tsakanin dan ci-rani don neman kudi da mai neman kariya. Amma ba a wata kasa ta EU za a yi wannan bincike ba. Lamarin ya ta da wata mahawara musamnman a bangaren doka. Domin duk mai neman mafakar siyasa a Jamus, dole ne ya gabatar da wannan bukata a cikin kasar. Saboda haka a ra'ayin Ska Keller da ke zama shugabar bangaren 'yan jam'iyyar The Greens a majalisar Turai, hakan nufin an binne 'yancin neman mafakar siyasa a tarayar Turai.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ajiye 'yan gudun hijrar a kasashe kamar Libiya wata matsala ce

Deutschland Bundeskanzlerin beim Weltflüchtlingstag
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Ta ce: "Abin da aka sa gaba a nan shi ne a tsare mutane a sansanoni a wasu kasashe irinsu Libya inda ba su da cikakkiyar kariya."

Wata matsalar ma ita ce dole a samu kasashen da ke za su shirin bude sansanonin a cikinsu. Tunisiya ga misali ta watsi da shi. A tsakanin kasashen EU ma ana fargaba cewa wadannan sansanoni ka iya dagula al'amura a kasashen da ba su tsaya kan kafufunsu ba. Masu goyon bayan shawarar sun ce da haka za a yi maganin masu fataucin dan Adam. Batun bude sansanonin tsare 'yan gudun hijira ba sabon abu ne domin tun a wasu shekaru da suka gabata wannan mataki ya samu goyon bayan tsohon ministan cikin gida na Jamus Thomas de Maizière da Sebastian Kurz da ke zama shugaban gwamnatin kasar Austriya a yanzu.

Ya ce: "Dole ka'idar mafi muhimmanci ta zama cewa duk wanda ya biyo barauniyar hanya dole a tsayar da shi a iyakokin waje na EU, inda za a kula da shi kana a koma da shi gida."

Yanzu akwai wasu kasashen kamar Faransa da Italiya da ke tunanin yiwuwar bude sansanonin. Ko shakka babu wannan shawarar za ta ci gaba da daukar hankali a takaddamar da ake yi tsakanin kasashen EU dangane da batun na 'yan gudun hijira.