1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin dubarun yaƙin nema zaɓe a Afirka

November 28, 2012

Hanyoyin da 'yan siyasa ke bi wurin cimma burinsu a Afirka sun canza sosai, bisa la'akari da sauye sauyen da nahiyar kanta ta samu ta hanyar amfani da kimiyya wurin faɗakarwa.

https://p.dw.com/p/16rAg
Hoto: Daniel Pelz

Burin kuma shi ne ta yadda za a kai ga taɓo matasa masu yawan gaske, kamar yadda aka yi la'akari da shi a zaɓen baya bayan nan da aka gudanar a ƙasar Saliyo.

Idan aka ɗauki misalin shugaba Yuweri Museveni na ƙasar Yuganda, a iya cewa, saƙonninsa na yaƙin neman zaɓe sun kasance tamkar wani abun sha'awa ne ga matasa inda suke amfani da waƙoƙinsa a cikin wuraren shaƙatawa da sauransu. A ƙasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, shi kuma ya fitar da wani sabon salo ne a karon farko a ƙasar inda a lokacin yaƙi neman zaɓe, ya shirya wasu ƙwallon ƙafa, abun da ya sa matasan suka ba shi laƙanin sunan "mafi cancanta" kamar yadda Leonard Balogum Korama shugaban yaƙin neman zaɓensa ke cewa.

"Suna ganinsa ne a matsayin mutumen da ya cancanci ya jagorancin ƙasar, wanda kuma suke wa kallon ingantaccen ɗan takara, hasali ma suna danganta shi ne da ɗan ƙwallon ƙafar nan Leonel Messi ko kuma Ronaldo, suna ma danganta shi da kasancewa ɗan ƙwallo mafi ƙwarewa a duniya, tun daga wannan lokacin ne muka ce to bari mu yi amfani da hakan a yaƙin neman zaɓen mu."

Su dai matasa sune al'umma mafi yawa a cikin ƙasashen Afirka, don haka ko shakka babu dole ne sai an dama da su, kuma hakan ba abun mamaki ne ba idan har yanzu 'yan siyasa suka mai da hankalinsu ga zawarcin su fiye da yadda ake zato.

Präsident von Uganda Yoweri Museveni
Shugaba Yoweri Museveni na YugandaHoto: dapd

Sanin kowa ne dai matasan sun fi kowane sashe na al'umma amfani da yanar gizo, ita ma wata kafa ce ga 'yan siyasar domin janyo hankullan su gare su inji Jerry Sam ɗan ƙasar Ghana, mai nazari kan yanayin yaƙin neman zaɓe a Afirka.

"Nahiyar Afrika yanki ne na matasa. A yanzu matasa sun fi rinjaye a ciki, sa'annan kuma su matasan ne suka fi amfani da yanar gizo tare da fahimtar junansu yasu yasu. Kenan dole ne akasarin 'yan siyasa su ma su ɗauko daidai da matasan domin su cimma burinsu. Me nene burin ɗan siyasa ya kai ga iko. Ni a nawa gani sai in ce idan har suka bi wannan hanyar sukan iya cimma burin nasu tun da matasan za su iya komawa gida su bayyana wa iyalansu manufa. Kuma hanya ce da ake iya bi wurin shimfiɗa mahawara a kan ingantaccen mulki."

Amfani da yanar gizo a wannan zamanin ya kasance wajibi ga jama'a domin komi ya koma sai da yanar gizo, wani ƙalubale ne kuma ga hukumomin Afirka ta yadda za su samar da hanyoyin ilmantar da miliyoyin matasansu domin su yi amfani da su.

A wani binciken da wata cibiyar na'urorin zamani ta yi a Najeriya, ta gano cewar, shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya samu ziyartar shafinsa na Facebook daga matasa sama da dubu ɗari bakwai a lokacin yaƙin neman zaɓe, kuma ta hanyar yanar gizo ce ya bayyana sakamakon zaɓen da ya lashe a shekara ta 2011.

DW_Nigeria_Integration2
Shugaba Jonathan ya buɗe shafin Facebook a zaɓen 2011Hoto: Katrin Gänsler

A ƙasar Kenya matasa sun yi wa firaministan ƙasar wani laƙanin suna a sunansu na Facebook, inda suke dangata shi da "Gwarzon Namiji" kai tsaye kuma sunan ya bi duniya cikin ɗan ƙanƙanen lokaci inji Dr. Carey Onyango wani mai nazarin al'amuran siyasar ƙasar.

"Hanya ce mai sauƙi sosai ta yadda za a taɓo adadin jama'a mai yawa cikin ɗan ƙaramin lokaci. Za ka iya amfani da yanar gizo ko ma ta hanyar wayar tarho, to amman yanar ta fi sauƙi, musamman ma idan har aka haɗa su gaba ɗaya."

Ba shakka yanzu dai ta bayyana a fili cewa yanar gizo ta kasance wani abu na daban wanda ya zama dole ga amfanin jama'a, ba kamar yadda ake masa kallo ba a 'yan shekaru bayan da suka wuce, wato yanzu yanar gizon ta kasance rigar zamani a saki a huta.

Mawallafa: Sarah Kamara / Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal