1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon bincike kan kwayar cutar Zika

Gazali Abdou TasawaMarch 1, 2016

Sakamakon wani binciken kimiyya da cibiyar bincike ta Pasteur da ke Faransa ta wallafa ya nuna cewa akwai alaka tsakanin Zika da cutar Guillain-Barre mai daskare jijiyoyi.

https://p.dw.com/p/1I4a8
Brasilien Zika CDC
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Penner

Sakamakon wani binciken kimiyya da cibiyar bincike ta Pasteur da ke a birnin Paris na kasar Faransa ta wallafa a wannan Talata a jaridar The Lancet ta Birtaniya, ya nunar da cewa akwai yiwuwar kwayar cutar Zika wacce ake fama da ita a yankin Kudancin Amirka da ke haddasa haifar jariri da nakasa ta kasance ummulhaba'isan haddasa cutar Guillain-Barre da ke kama jijiyoyin jikin dan Adam.

A cewar Parfesa Arnaud Fontanet jagoran cibiyar nazarin cututtukan annoba ta Pasteur, sakamakon binciken da suka yi kan kwayar cutar ta Zika ya nunar da cewa akwai alaka sosai tsakanin kwayar cutar da zika da kuma wannan matsala ta daskarewar jijiyoyin jikin dan Adam.