1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kundin tsarin mulki a Tunisiya

LateefaJanuary 27, 2014

Majalisar dokokin kasar Tunisiya ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar, da aka kwashe tsahon shekaru biyu ana fitar da daftarinsa.

https://p.dw.com/p/1AxaQ
Hoto: Reuters

Bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar, Firaministan rikon kwaryar Tunisiya Mehdi Jomaa ya sanar da sabuwar gwamnati da za ta jagoranci kasar zuwa gudanar da zabuka a karshen wannan shekarar da muke ciki.

Jomaa ya dare kan karagar mulkin kasar ta Tunusiya a matsayin Firaministan rikon kwarya, bayan da jam'iyyar Ennahda ta amince ta sauka daga kan karagar mulki biyo bayan yarjejeniyar da suka cimma da 'yan adawa sakamakon kwashe tsahon watanni ana zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a kasar.

Sabon kundin tsarin mulkin da 'yan majalisun dokokin kasar ta Tunisiya suka amince da shi dai shi ne irinsa na farko tun bayan juyin-juya halin da ya afku a kasar a shekara ta 2011 da yayi awon gaba da gwamnatin Zine El-Abidene Ben Ali na Tunisiyan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh