1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kwamitin nazarin badaƙalar man fetir a Najeriya

November 16, 2012

Ƙasa da tsawon makonni biyu da miƙa rahoton kwamitin Nuhu Ribadu game da almundahana da arzikin man fetur gwamnati ta kafa sabon kwamitin binciken rahoto.

https://p.dw.com/p/16kjN
Hoto: AP

Bisa ga dukkan alamu ana sake shirin kai ruwa bisa rana a tsakanin gwamantin Najeriya da ta sake kafa wani kwamiti don nazarin rahoton Nuhu Ribadu da kuma 'yan adawa da kungiyoyi na farar hular dake cewar wai mu gani a ƙasa inji karen da ake biki a gidansu.

An dai ambato sunan manya an kuma ce an ci kuɗi a rahoton kwamitin Mallam Nuhu Ribadu da gwamantin ƙasar ta kafa domin binciken badaƙalar man fetur ɗin dake zama ɗaya daga cikin mafi girma a tarihin Najeriya da kuma yanzu haka ke ɗaukar hankali da jawo kace nace a ciki da ma wajen ƙasar a tsakanin masu kallon rahoton a matsayin wani gagarumin ci-gaba da kuma waɗanda suke ganin an yi kuskure amma wuce gona da iri.

Ƙoƙarin daɗaɗa wa talakawan ƙasa

To sai dai kuma a wani abun dake zaman ƙoƙarin ba maras ɗa kunya gwamantin tarayyar Najeriya ta yi watsi da kace nacen 'yan ƙasar da ma bakinta tare da kafa wasu jerin kwamitoci da nufin nazarin rahoton da ya ambato yadda kamfanonin mai da jami'an gwamantin ƙasar da kuma masu ruwa da tsaki da masana'antar man ƙasar suka riƙa cin karen su babu babbaka na lokaci mai tsawo.

Sabon kwamitin da ya ƙunshi ministocin gwamantin ƙasar huɗu ƙarƙashin jagorancin ministan kodagon Emeka Wogu dai ne ke da alhakin nazarin batutuwan da rahoton ya taɓo, da fitar da farar takarda domin aiki a cikin makonni biyu masu zuwa.

Nigeria Nuhu Ribadu Präsidentschaftskandidat
Sake duba rahoton Nuhu RibaduHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A baya dai an kai ruwa rana a tsakanin jami'an gwamantin da 'yan uwansu dake ma'aikatar man fetur ɗin ƙasar dake zargin shugaban kwamitin da gaza tabbatar da cikakken bincike, da kuma jam'iyun adawar ƙasar da ma ƙungiyoyi na farar hular dake zargin gwamnatin da ƙoƙari na ɓoye gaskiya.

To sai dai kuma daga dukkan alamu shi kansa sabon kwamitin ya gaza burge 'yan adawar da suka ce gwamantin ba da gaske take ba a kokarin ganin bayan rashawar da ta yi katutu kuma ke barazana ga makomar masana'antar man.

Sama da kaso 85 cikin 100 na arzikin Najeriya dai na zuwa ne daga baƙar hajjar ta mai da yanzu haka ke zaman kafa ta wasoso da wa kaci ka tashi da dukiyar al'ummar ƙasar.

Facaka da kuɗin mai da iskar gas

Sama da trillion hudu ne dai rahoton yace an kwashe daga iskar gasa ɗin da kasar ke hakowa a cikin shekaru 10 da suka gabata banda kuma karyar da farashin man domin amfanin manyan kamfanonin haƙar sa dake waje.

Rahoton dai ya kuma ce Najeriya ce kaɗai ke sai da man ta ga dillallai maimakon ƙasashe da kamfanonin dake bukatar sa kai tsaye, abun kuma da ya haifar da al'adar kamasho ta shafaffu da mai cikin ƙasar.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Rub da ciki da kuɗin maiHoto: Getty Images

Mahukuntan na Abuja dai na ƙoƙarin ganin ƙasar ta kawo ƙarshen annobar cin hancin da ta yi aure ta tare ta kuma mai da ƙasar kurar baya tsakanin masu taƙama da arzikin na mai.

Mallam Garba Umar Kari dai na zaman masani ga batun cin hancin ƙasar ta Najeriya, kuma a cewar sa da kamar wuya a kai ga samun sauyin da 'yan ƙasar ke fatan gani a yanzu haka.

Sama da dallar Amurka milliyan dubu 400 ne dai suka bi ruwa a tsakanin shugabanni da 'yan uwansu 'yan kasuwa da 'yan boko a cikin shekaru 13 na sake dawowar demokraɗiyya a ƙasar ta Najeriya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani