1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a Afirka ta Tsakiya

Mohammad AwalSeptember 9, 2013

Ga dukkan alamu har yanzu a kwai sauran rina a kaba a Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya, watanni 6 bayan da 'yan tawayen Seleka suka yi juyin mulki a kasar.

https://p.dw.com/p/19eRc
Hoto: picture-alliance/dpa

Dakarun kasar Afirka ta Tsakiya na kokarin fatattakar 'yan tawaye da ke goyon bayan tsohon hambararren shugaban kasar Francois Bozize, a rana ta biyu da ake ci gaba da gwabza fada da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 60.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan sabon rikici na daya daga cikin fada mafi muni, tun bayan da dakarun 'yan tawaye na Seleka suka hambarar da gwamnatin Shugaba Bozize sakamakon juyin mulkin da suka yi a watan Mayun da ya gabata.

Wannan sabon fadan dai ya barke ne a ranar Lahadi a garin Bossangoa, mahaifar tsohon Shugaba Bozize kimanin Kilomita 250 da arewacin babban birnin kasar Bangui, bayan da masu tada kayar baya da ke goyon bayan Bozizen suka farma kauyukan da ke makwabtaka da Bossangoa, tare da lalata gadoji da kuma sauran kayan more rayuwar al'umma.

Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa masu tada kayar bayan na daukar fansa a kan tsirarun mabiya addinin Musulunci bayan da aka rantsar da shugaban 'yan tawayen Seleka da suka hambarar da gwamnatin Bozize, Michel Djotodia a matsayin shugaban kasa Musulmi na farko a kasar da Kiristoci ke da rinjaye.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal