1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon salon Biritaniya game da Iraƙi

Ibrahim SaniDecember 10, 2007
https://p.dw.com/p/CZY5

Faraministan Biritaniya Godon Brown ya kai wata ziyarar ba zata izuwa Iraƙi. Jim kaɗan da isarsa, Mr Brown ya wuce kai tsaye izuwa garin Basra, don ziyartar dakarun sojin ƙasar dake gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya. Kafafen yada labarai sun rawaito Faraministan na cewa nan da ´yan makonni kaɗan, sojin na Biritaniya za su miƙa ragamar harkokin tsaro na yankin hannun Jami´an sojin Iraqi. Mr Godon Brown ya yaje ƙasar ta Iraƙi ne jim ƙadan bayan ya ɗaukaka kiran sako ´Yan Biritaniya biyar ɗin nan da akayi garkuwa da su. Mr Brown ya kuma yi watsi da sharaɗin waɗanda su ka yi garkuwa da sun da cewa abune da ba zai taɓa yiwuwa ba. Ma su garkuwar dai sun buƙaci Biritaniya janye sojinsu ne daga Iraqi, a matsayin sharaɗin sako ´Yan ƙasar biyar da akayi garkuwa da sun.