1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon tsarin mulkin Masar ya fara aiki

December 26, 2012

Shugaban ƙasar Masar Mohamed Mursi ya rantaba hannu kan sabon kundin tsarin mulki

https://p.dw.com/p/179FM
Hoto: Reuters

Shugaban ƙasar Masar Mohamed Mursi ya saka hannu kan sabon kundin tsarin mulki, wanda ya ce zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin siyasan ƙasar, tare da kawo cigaban tattalin arziki.

Sakamakon zaɓen ya nuna kusan kashi 64 cikin 100 na waɗanda su ka kaɗa ƙuri'a, sun amince da sabon kundin, wanda 'yan adawa su ka ce ya na cike da ra'ayin 'yan ƙungiyar 'yan uwa Musulmai, masu goyon bayan shugaban. Akwai mutane masu yawa da su ka ƙaurace kaɗa ƙuri'a kan kundin, saboda taƙaddama bisa abubuwan da ya ƙunsa.

A wani labarin Majalisar Dattawan ƙasar ta Masar da ake kira Shura, ta fara zama sakamakon amincewa da kuma rattaba hannu da shugaban ya yi akan sabon kundin tsarin mulkin. Majalisar ta ƙunshi mutane 90. Kuma ita ce zata tsara dokoki kafin zaɓen sabbin 'yan majalisu nan da watanni biyu masu zuwa, da kuma dokokin yadda za a yi zaɓen.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi