1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin warware rikicin Mali

December 20, 2012

MDD za ta jefa kuri'ar yin na'am da tura dakaru zuwa Mali, wadda ke fama da rikicin siyasa da na 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/175yX
Members of the United Nations (UN) Security Council vote extend the mandate of the UN mission in Libya at UN Headquarters in New York March 12, 2012. REUTERS/Lucas Jackson (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: REUTERS

Jami'an diflomasiyya sun sanar da cewar a wannan Alhamis ne kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai jefa kuri'ar amincewa da kudirin da zai bada damar tura dakarun kungiyar tarayyar Afirka zuwa kasar Mali domin shirya kaddamar da hari akan mayakan da ke da alaka da kungiyar AlQa'ida. Dama da yammacin Larabar nan ce Faransa za ta tura tsarin kalmomin da ta ke son a yi anfani da su wajen tsara dafarin, zuwa ga mambobi 14 na kwamitin sulhun.

Kasar ta Faransa dai ta yi tsawon makonni tana tattaunawa tare da jami'an Amirka akan batun. Sai dai jami'an diflomasiyyar Amirka sun nuna ta'ba'ba game da ko rundunar da tarayyar Afirka ke shirin turawa zuwa kasar ta Mali za ta sami karfin yaki, da kuma yin galaba akan mayakan AQIM da ke zama reshen AlQa'ida ne a yankin Maghrib, da kuma na kungiyar MUJAO da ke fafutukar kaddamar da jihadi a yankin yammacin Afirka.

Idan za'a iya tunawa dai tun cikin watan Maris ne mayakan suka kwace iko da yankin arewacin kasar ta Mali, yankin da kuma fadin sa ke zama rabin kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu