1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dokar 'yan gudun hijira a Isra'ila

Yusuf BalaOctober 7, 2014

Dubban 'yan gudun hijira daga kasashen Afrika daban-daban ke shiga kasar Isra'ila ta barauniyar hanya, wadanda gwamnati kan kama su kwase shekaru a gidan kaso.

https://p.dw.com/p/1DRZy
Palästina Blockade Gazastreifen Grenze zu Israel Grenzzaun
Hoto: Imago/UPI Photo

Ministocin Isra'ila na tattaunawa a ranar Talatannan kan sabuwar doka kan yadda za ta hukunta masu shiga kasar ta barauniyar hanya daga kasashen Afrika, bayan da babbar kotun kasar ta haramta gwamnati na kama 'yan gudun hijirar tana daurewa ba tare da gurfanar da su a gaban kuliya ba.

Wannan tattaunawa ta Firayin minista Benjamin Netanyahu da ministan harkokin shari'a da ministan harkokin cikin gida da harkokin tsaro na zuwa ne bayan da mambobin majalisar dokokin kasar suka tafka wata muhawara mai zafi da ke sukar hukuncin wannan kotu.

Ministan harkokin cikin gida mai barin gado Gideon Saar ya ce umarnin kotun ya haramta wa gwamnatin kasar daukar hukuncin a hannun ta a dangane da batun na kwarar bakin na Afrika.

A hukuncin kotun na ranar 22 ga watan Satumba, ya nunar da cewa Isra'ila ba ta da ikon kama dan gudun hijira da ya shigo mata kasa ba bisa kaida ba ta kulle sama da tsawon shekara daya ba tare da an kai shi gaban kuliya ba, inda ta bada umarnin rufe cibiyar kulle irin wadannan 'yan gudun hijira ta Holot cikin kwanaki 90.

Kimanin yan gudun hijira 2,000 ne daga kasashen Afrika daban-daban a yanzu a ke tsare da su a wannan cibiya da ke kudancin saharar Negev.