1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon wucin gadi na zaben Madagaska

December 21, 2013

Dan takara da gwamnati ta tsayar Hery Rajaonarimampianina na kan gaba a zaben shugaban kasar Madagaska da ya gudana a ranar Jumma'a.

https://p.dw.com/p/1AeR0
Wahlen Madagaskar Hery Rajaonarimampianina
Hoto: RIJASOLO/AFP/Getty Images

Hukumar zabe mai zaman kanta ta tsbirin Madagaska ta bayyana sakamakon wucin gadi na zaben da aka gudanar a runfuna 188 daga cikin runfuna dubu 20 da aka kada kuri'a a cikinsu a fadin kasar. Bisa ga wannan kiyasi dai dan takara da gwamnatin da ke ci a yanzu ke goya wa baya wato Hery Rajaonarimampianina ne ke gaban inda ya zuwa yanzu ya lashe kashi 50,43% na kuri'un da aka kirga. Yayin da shi kuma Robinson Jean Louis wanda ke samun goyon bayan tsohon shugaban kasa Marc Ravalomanana, ya lashe kashi 49,17% na kuri'un da aka riga aka kirga.

Ita dai hukumar zabe mai zaman kanta ta Madagaska ta bayyana cewar za a sami cikakken sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasa kan nan da karshen shekara. Masu sa ido sun nunar da cewar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da kuma na 'yan majalisa ya gudana ba tare da wani tashin hankali ba a ranar Jumma'a.

Wannan dai shi ne karon farko da aka shirya zabe a Madagaska tun bayan da sojoji suka taimaka wa Andry Rajoelina hambarar da gwamatin Marc Ravalomanana.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal