1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren MDD ya yi kira ga ɓangarorin sudan su nuna halin Dattako

September 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuB2

Sakatare janar na Majalisar ɗinkin duniya Ban Ki-Moon yayi kashedin cewa karuwar tashe tashen hankula dake faruwa a kwanannan a yankin Dafur ka iya kawo cikas ga nasarar taron sulhu wanda ake fatan zai kawo ƙarshen hargitsin yankin na yammacin Dafur da ya shafe tsawon shekaru hudu yana gudana. Ban Ki-Moon yace yayi mamaki matuƙa da rahotannin da ya samu cewa an kai harin na baya bayan nan ne bayan da gwamnatin Sudan a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa a lokacin ziyarar da ya kai zuwa Sudan a wannan watan, ta jaddada ƙudirin tsagaita wuta a Dafur, gabanin taron Libya da zaá yi a ranar 27 ga watan Oktoba. Sakataren Majalisar ɗinkin duniyar ya sake yin kira da babbar murya ga dukkan ɓangarorin su nuna sanin ya kamata su tsagaita faɗa domin samun wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.