1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Jiragen sama sun dawo jigila

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 8, 2020

Najerriya ta sake bude filayen jiragen sama na Abuja da Lagos a Larabar wannan makon, bayan kwashe fiye da watanni uku a rufe sakamkon annobar cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3eypu
Nigeria Flughafen Abuja | Coronavirus | Wiedereröffnung
Filin jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke Abuja NajeriyaHoto: DW/U. Abubakar Idris

Jirage dai sun ta sauka suna tashi tsakanin Abuja da Lagos da ke zaman manyan birane biyu na Najeriyar, abin da ke nuna kara sassauta matakan da aka dauka a kan annobar cutar coronavirus a kasar. An dauki matakai sosai kama daga karnuka da ke sinsina jakunkunan matafiya ya zuwa tilasta bayar da tazara. 

Alhaji Rabiu Yadudu shi ne shugaban tashohin jiragen saman Najeriyar, ya kuma ce sun dauki matakai masu yawa: "Dama fargabar kowa shi ne ya zo filin jiragen sama ya kamu da cuta bayan ya bar gidansa lafiya. Matakan da muka dauka shi ne tabbatar da cewa mutum ya shigo filin jirgin saman lafiya kuma ya fita lafiya ba tare da ya kamu da wannan cutar ba. An dauki matakin bayar da tazara har a cikin jiragen, inda aka tsallake kuje a atsakanin fasinjoji domin kaucewa yaduwar cutar."

Nigeria Flughafen Abuja | Coronavirus | Wiedereröffnung
Bayar da tazara yayin tantance fasinjojiHoto: DW/U. Abubakar Idris

Fasinjoji dai na cike da murna da kai wa ga wannan rana da suka sake samun dama ta shiga jirgin saman domin ci gaba da harkokinsu na kasuwanci ko kuma na karatu, koda yake sun yi korafin cewa an kara kudin tikiti, inda suka bukaci da a yi nazari domin saukakawwa al'umma ganin halin matsin tattalin arziki da suka tsinci kansu a ciki sakamakon annobar ta coronavirus. Fasinsojoin dai sun kuma nunar da cewa akwai bukatar samar da na'urar busar da hannaye bayan mutum ya wanke hannunsa, sai dai sun yaba da  matakan da aka dauka na bayar da tazara a tsakanin fasinjojin. 

An dai tsara cewa ranar 11 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, za a bude karin filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal da Owerri yayin da za a bude sauran a ranar 15 ga watan na Yuli. Har yanzu dai ba a bayyana ranar da za a bari jirage daga kasashen waje su  ci gaba da yin jigila a Najeriyar ba.