1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salva Kiir na fiskantan matsi daga duniya

Usman Shehu UsmanAugust 26, 2015

A yau Laraba ne shugaban kasar Sudan ta Kudu ake jiran ya sa hannu bisa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsa da abokan gaba, don kawo karshen yakin basasan kasar

https://p.dw.com/p/1GLZp
Südsudans Präsident Salva Kiir Mayardit
Hoto: Reuters

Sa-hannun fatan da ake yi shi ne ya kawo karshen tashin hankali da aka fara kusan shekaru biyu, inda dubban mutane suka mutu, wasu sama da miliyan biyu suka rasa gidajensu. Tun kusan kwanaki 20 da suka gabata madugun 'yan tawayen Riek Macher ya sanya hanu kan yarjejeniyar, yayinda shi kuwa Salva kiir ya ce akai masa takardun ya yi nazari kafin sa hannu. Amirka dai a yanzu ta sa kahon zuka kan Juba, inda Amirkan ta gabatar da wani kuduri mai tsanani kan Sudan ta Kudu, wanda zai hada da hana sayar mata da makamai, muddin shugaba Salva kiir ya ki sa hannu.