1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da aiki a Najeriya da keken napep

January 18, 2017

A Najeriya wani matashi da ya kamala karatun jami'a ya kasance mai tasiri ga alumma ta hanyara samawa kansa aikin yi da ma wasu matasan fiye da 400 ta hanyar sana'ar Keke Napep a Abuja hedikwatar Najeriya.

https://p.dw.com/p/2VzKz
Nigeria Abuja Benzinpreis
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Matashi Babagana Abba daya ne daga cikin mutanen da za ace rikicin Boko Haram da ya shafi yankin da ya fito na Dallori a Jihar Borno ya jefa shi ciki hali na tagayyara musamman bayan fafutukar da ya yi na kamala karatun jami'a kuma ya tsinci kansa a yanayi na rashin aikin yi, to sai dai maimakon haka sai ya kukuta ya samu sayen Keke-Napep a Abuja don ya gwada, gwajin da ya sa harkar ta karbe shi har ya kai ga samar wa matasa da dama aikin yi. Shin me ya ja hankalinsa ne ya ki yarda da zaman kasha wando kaman sauran matasa?

Dama a kan ce himma ba ta ga rago domin kuwa da haka Babagana Abba da ya karanta sashin injinya a matsayin digiri ya ci gaba da samun bunkasa a wannan sana'a har ma ta kai shi ga jawo hankali wasu abokansa da suka zuba jari ta hanyar sayen keke napep suna ba shi ya kula masu, inda ya kai ga kafa kamfani na musamman don wannan harka a Abuja. Hajia Safiya Usman na cikin mutanen da suka zuba jarrinsu.

Na nemi jin ta bakin wasu matasa da suka amfana da wannan tsari da baya ga aikin yi sun ma kai ga mallakar keke napep na kansu a Abuja.

Irin tasirin da wannan matashi ke yi a cikin al'umma ta fanin dogaro da kai da samar da aikin yi ga dimbin matsa abin koyi ne ga dimbin matasa da ya kamata su yi watsi da dogaro kacokan a kan gwamnati ta sama masu aikin yi, dama ai babu maraya sai rago.