1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Samar da hanyar raba bakin haure

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 23, 2019

Kasashen Jamus da Faransa da Italiya da kuma Malta, sun amince da rarraba bakin hauren da aka ceto daga Tekun Bahar Rum, a kokarin da suke na shiga Turai a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/3Q7TG
Malta EU-Treffen der Innenminister | Horst Seehofer, Deutschland
Ministan harkokin cikin gida na Jamus Horst SeehoferHoto: Getty Images/AFP/M. Mirabelli

Ministan harkokin cikin gida na Maltan Michael Farrugia ne ya bayyana hakan, inda ya ce shi da takwaransa na Jamus Horst Seehofer sun amince da yarjejeniyar da za a gabatar domin tattaunawa yayin taron ministocin cikin gida na kasashen kungiyar EU a ranar takwas ga watan Oktoba mai zuwa. Sai dai ya ce amincewar tasu ba za ta yi amfani ba, matukar ba a fadada abin domin amincewar sauran kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar turai EU ba. Shi ma a nasa bangaren ministan cikin gida na Jamus din Horst Seehofer ya sanar da cewa tsarin zai kasance na watannin shida, kuma za a kaddamar da shi da zarar sauran kasashen kungiyar ta EU sun amince.