1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Langsam hilft Europa Mali

October 24, 2012

Duk da cewa ƙasashen Turai sun bayyana aniyarsu ta taimaka wa ƙoƙarin ƙasashen Afirka na magance rikicin Mali, har yanzu sun kasa fayyace irin taimakon da za su bayar.

https://p.dw.com/p/16Ven

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce kasarsa a shirye ta ke ta bayar da gudunmawa wajen inganta harkokin tsaro a ƙasar Mali. Sai dai ya ce ba za ta bayar da gudunmawar makamai ko na sojoji domin fattatakar masu kaifin kishin addinin Islama daga arewacin ƙasar ba. Guido Westerwelle ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana a birnin Berlin da manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Sahel wato Romano Prodi.

Manyan jami'an biyu sun tattauna game da tallafin da Jamus za ta bayar wajen horas da jami'an tsaron ƙasar Mali dabarun yaƙi. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bayyana halin da ake ciki a Mali da cewa abin damuwa ne matuƙa, domin masu kishin addinin Islama na keta haƙƙin ɗan Adam, ana tauye 'yancin mata da lalata wuraren tarihi na Islama a arewacin ƙasar.

Westerwelle ya ci gaba da bayani cewa kamata yayi Turawa dake tambayar shin me ya haɗa su da ƙasar Mali da har za su nuna damuwa da cewa iyakar ƙasa ɗaya za ka tsallake ka shiga tekun Bahar Rum, saboda haka idan arewacin Mali ta ruguje to fa nahiyar Turai gaba ɗaya za ta fuskanci barazana ta 'yan ta'adda.

Westerwelle Prodi
Hoto: AFP/Getty Images

"Idan aka kafa makarantun 'yan ta'adda a can, idan aka kafa sansanin 'yan ta'adda na duniya a can, wannan barazana ce ga arewacin Mali da ƙasashen Afirka kaɗai ba, haɗari ne gare mu a Turai. Da wannan gudunmawar da za mu bayar za mu kare kanmu, za mu daidaita al'amura a Mali, za mu kare nahiyar Turai daga ayyukan ta'addanci da hare hare."

Halin da ake ciki a Mali yana da hatsari

A nasa ɓangaren wakili musamman na babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Sahel, Romano Prodi ya nuna cewa halin da ake ciki a Mali babbar barazana ce ga ilahirin yankin Sahel, musamman saboda rashin tsaron kan iyakokin ƙasashen wanda haka ka iya samar da wani makeken yanki ga ayyukan 'yan ta'adda. Prodi wanda shi ne tsohon shugaban hukumar tarayyar Turai kuma tsohon Firaministan Italiya ya ce tuni ya tattauna da shugabannin ƙasashen gamaiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, wadda ke matsa ƙaimin ganin an fatattaki masu kishin Islama daga arewacin Mali. A ganawarsa da Westerwelle ya yi ƙoƙarin ganin an jinginar da batun tsoma bakin soji yana mai cewa a matsalolin Mali a matakin farko na da nasaba da siyasa da ƙabilanci wanda ba za a iya magancewa da bakin bindiga ba.

"Ko kaɗan ba za a iya amfani da katsalandan soji daga Turai don magance wata matsala da gaba ki ɗayanta Afirka ta shafa. Muhimmin abu shi ne samar da kyakkyawan shugabanci a Mali, da zai zama kyakkyawan misali ga ilahirin yankin."

Warware rikicin a siyasance ya fi muhimmanci

Manyan jami'an biyu sun ce ta hanyar siyasa ce za a iya samar da dauwamammen zaman lafiya da zai ba da la'akari ga buƙatun dukkan 'yan ƙasar. A ranar 22 ga watannan na Okotoba ministocin harkokin wajen ƙasashen tarayyar Turai sun yanke shawarar tallafa wa ƙoƙarin ƙasashen Afirka na magance rikicin Mali. Sai dai Westerwelle ya kawar da yiwuwar tura jiragen saman yaƙin Turai Mali.

Al-Kaida im Islamischen Maghreb
Ƙungiyoyin kishin Islama na cin zarafin bil Adama a arewacin MaliHoto: AFP/Getty Images

Ƙasashen yammacin duniya na nuna fargaba game da rikiɗewar arewacin Mali zuwa cibiyar shirya ayyukan ta'addanci a Afirka. Majalisar Ɗinkin Duniya ta na jiran kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi mata bayyani dalla dalla game da hanyoyin da za ta bi wajen karɓe arewacin Mali da hannu masu tsananin kishin addinin Islama.

Mawallafa: Peter Stützle / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu