1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkewar harkokin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniNovember 19, 2007
https://p.dw.com/p/CIlc

Ma´aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi tofin Allah tsine ga kiran da Amirka ta yi wa ƙasar na martaba dokokin ƙasa. A cewar mahukuntan na Pakistan, wannan ba sabon abu bane, domin a cewarsu sun daɗe a kann wannan tsari. Bayanin hakan ya zo ne bayan ganawar shugaba Musharraf da kuma mataimakin sakataren harkokin waje na Amirka Mr John Negroponte.Tattaunawar shugabannin biyu ta mayar da hankaline,

kann dokar ta ɓaci da kuma zaɓen gama gari da ake shirin gudanarwane a ƙasar.Wakilin na Amirka na ƙokarin samo bakin zaren warware rikicin siyasane da ƙasar ta faɗa a ciki, bayan Mr Musharraf ya ƙaƙabawa ƙasar dokar ta ɓaci. A yanzu haka dai Amirka na bukatar Mr Musharraf da shugabar adawa ta ƙasar Benazir Bhutto komawa teburin sulhu, bisa manufar cimma buƙatar da aka sa a gaba. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito Bhutto na adawa da wannan shiri.