1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sasanta rikicin Sudan ta Kudu

January 2, 2014

Gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa bangarori biyu na Sudan ta Kudu dake gaba da Juna za su zauna kan teburin shawara Addis Ababa babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1AkYi
Hoto: Reuters

Ministan kula da harkokin wajen Habashan dake shiga tsakanin a rikicin na Sudan ta Kudu, Dr. Tedros Adhanom ya ce ko da shike tuni tawagogin bangarorin biyu suka isa birnin na Addis Ababa domin tataunawar, amma ba za a fara tattaunawa ta kai tsaye domin cimma yarjejeniya ba, sai a cikin kwanaki masu zuwa. Sai dai kuma duk da kokarin da kasar ta Habashan ke yi na kawo sassan da ke cikin rikicin akan teburin shawara, ci gaba da gwabza yaki a wasu sassa na Sudan ta Kudu na dushe manufar shiga tsakanin.

Kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Habasha Dina Mufti, ya yi karin haske a kan batutuwan da taron na birnin Addis Ababa zai mayar da hankali akai.

Ya ce " Muhimman batutuwan da tattaunawar za ta mayar da hankali a kansu dai tuni kungiyar ci gaban kasashen gabashin Afirka ta IGAD ta tsara su. Na farko shi ne tsagaita bude wuta. Na biyu kuma shiga tataunawa ta kai tsaye, kana na uku kuma bude kofar kai agaji ga jama'a domin dimbin fararen hula ne suka tsere daga matsugunansu. Tilas a kula da jin dadin rayuwa da kuma hakkinsu."

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da yunkurin.

A tsokacin da ta yi dangane da wannan ci gaban, wakiliyar musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta tura zuwa Sudan ta Kudu, Hilde Johnson, ta ce kyakkyawar alama ce ta samun mafita, amincewar da bangarorin biyu suka yi na tura wakilan nasu domin sasanta tsakanin juna, bayan tashe tashen hankulan da suka tilastawa fiye da mutane dubu 200 tserewa daga matsugunansu.

Ta ce "Mun ga mummunar ta'asar da aka tafka a makwanni biyun da suka gabata. An yi ta kashe kashen rashin imani, da take hakkin dan-Adam. A kwai hujjar da ke nuna kabilanci a yadda yakin ke tafiya, wanda kuma ka iya wargaza tubalin gina jaririyar kasar."

Konflikt im Südsudan Flüchtlinge 30.12.2013
Hoto: picture-alliance/AP

Fadan kabilanci ake gwabzawa a kasar.

A fili take dai cewar, fadan na Sudan ta Kudu na nuna irin takaddamar da ke tsakanin manyan kabilun kasar guda biyu, wato kabilar Dinka ta shugaba Salva Kiir da kuma kabilar Nuer ta tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, inda hatta a baya bayannan ma shugaba Salva Kiir ya ayyana dokar ta baci a jihohin Unity da Jonglei, wadanda dakarun da ke biyayya ga Machar din ke da iko da manyan biranensu. Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu Hilde Johnson, ta ce abin da suka sa a gaba shi ne hana rikicin kara rincabewa.

Konflikt im Südsudan Flüchtlinge 31.12.2013
Hoto: picture-alliance/AP

Ta ce " Muna kokarin kawar da hatsarin ruruta wutar rikicin. A kan wannan dalili ne muke bukatar samun karin dakaru, kuma saboda haka ne muka shiga cikin yankunan, domin dakarunmu su sami damar kula da tsaro da kuma taimakawa mutanen da ke samun mafaka a sansanonin."

Johnson ta ce ala tilas ne dakarun na Majalisar Dinkin Duniya suka rungumi aikin binciken gano ko a kwai makamai a sansanonin domin tabbatar da cikakkiyar kariya ga wadanda ke samun mafakar, a dai dai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a tsakanin bangarorin biyu dake gaba da juna.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Mohammad Nasiru Awal/ LMJ