1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hajjin Bana cikin annobar coronavirus

Mahmud Yaya Azare LMJ
July 30, 2020

A karon farko, mahajjata a Saudiya sun yi hawan Arfa da ke zama babban rukunin aikin hajji, cikin yanayin walwala da sakata, sakamakon karancin da suke da shi, saboda annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3gCJt
Saudi-Arabien Mekka | Corona & Hadsch | Pilgerfahrt
Matakan bayar da tazara yayin hawan ArfaHoto: Getty Images/AFP

Mahajjatan da basu wuce 10.000 ba wadanda suka isa farfajiyar filin na Arfa cikin safa safa, bakuna da hancinsu na cikin takunkumi. Sanye da farin haramin da aka sakawa sinadarin kashe cututtuka  da hana jikewa, karancinsu ya bai wa galibinsu damar samun hawa dutsen na Arfa, wanda a baya sai mai tsananin rabo ne ke samun isa kansa.

Limamin da ya yi jagoranci sallar Azahar da La'asar da ake hadesu  a Masallacin Namirah da ke farfajiyar dutsen na Arfa, Sheikh Abdallah Almanee kira ya yi ga al'ummar Musulmin duniya da su tunkari masifun da ke fuskantarsu da ma sauran duniya da yin hakuri da dangana  da kuma yawan addu'oi ba kakkautawa: "Yana daga cikin  siffofin masu tsoron Allah, su rinka rungumar kaddara, komin dadi ko rashin dadinta. Amma hakan ba ya nufin nade hannu da rashin yunkurin tunkarar matsaloli da cutattukan da Allah ya kaddara za su same mu. Manzon Allah SAW, ya wajabta mana neman magani da daukar matakan rigakafi, kamar yadda ya wajabta mana yin addu'a domin waraka ga Allah take ba ga maganin da muke sha ba. Mu yi addu'a Allah ya yaye mana bala'i da dukkanin annoba da tsananin rayuwa da aikata sabo a fadin duniya. Ya kuma zama wajibi mu daina zatan wasu ne suka dora mana bala'i, domin tun ran gini ranar zane. Inda duniya za su taru kan su cutar da kai, ba za su isa yin komai ba, sai da yardar Allah."

A wannan Alhamis din ne Mahajjatan ke wucewa Musdalifa daga Arafa, inda za su kwana a filin Allah-Ta'ala domin kimtsawa rukunan karshe na aikin hajjin da suka hada da jifan shaidan da hawan Safa da Marwa.