1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harshen Hausa na fuskantar kalubale na zamani

Muhammad Waziri Aliyu AH
June 30, 2020

Al'adar karance-karance ta ja baya a wannan zamanin musamman ma a tsakanin Hausawa ta la'akari da yadda mafi akasarin jama'a suka fi karkata zuwa ga kallo da sauraro. Wannan shi ne batun da shirin Taba ka Lashe ya duba.

https://p.dw.com/p/3eYfX
audio_on_demand_hausa.gif

Harshe ko yare yana dorewa ne matukar masu yaren na wallafa shi ta hanyar gudanar da rubuce-rubuce bisa ka'idarsa. Kasancewa hakan ne zai ba da dama ga 'yan baya su fahimci yaren. Harshen Hausa yana daya daga cikin yaren da yake da yawan masu magana da shi musamman ma a yankin kasashen Afirka ta Yamma. Najeriya kuma ta kasance inda Hausawan suka fi yawa, sannan kuma akwai marubuta na harshen da dama. Sai dai yawan kallo da sauraro na kafofi na iya zama babbar barazana ga Hausar a cewar masana.

Rubuce-rubuce na zaman tubali na raya harshe sai dai zamani ya kawo sauyi

China Produktion von Karl-Marx-Anime in Hangzhou
Hoto: Getty Images/AFP

A Jihar Bauchi akwai wani shahararren marubucin wanda ya rubuta littattafai da dama domin bunkasawa da raya harshen na Hausa. A shekarun baya ana iya cewa rubuce-rubuce suna da matukar tasiri a tsakanin al'umma domin kuwa magabata a wancan zamanin ba su dauki lamarin da wasa ba kasancewar a kan dora manyan gobe bisa turbar karance-karance wanda hakan ke sa su taso cikin sha'awar karatu sosai. Sai dai kuma sannu a hankali zamani ya sauya, inda kallo da sauraro suka shigo kuma suka yi matukar tasiri a kan al'ummar Hausawa wanda hakan kuma ya zamo babban kalubale ga marubuta, domin kuwa wadannan abubuwa biyu sun kawo koma baya ga dabi'ar karance-karance a kasar Hausa.