1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauraron shari'ar Oscar Pistorius

March 3, 2014

Shahararren dan gudun fanfaleken kasar Afirka ta Kudu mai kafafun roba Oscar Pistorius ya musanta zargin da ake yi masa na kashe budurwarsa a shekarar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/1BIfn
Hoto: Reuters

A shari'ar da aka fara sauraro a Pritoria babban birnin kasar Afirka ta Kudun, wadda ba a nuna baki dayan ta kai tsaye a kafafen yada labarai ba, Pistorius ya ce bai kamata a tuhume shi da kashe budurwarsa Reeva Steenkamp ba inda ya ce ya ji motsi ne a bandakinsa wanda kuma hakan ya sanya shi yayi tunanin wani ne ya zo cutar da su shi da Reeva kuma shine dalilin da ya sanya shi yayi harbin da ya hallaka ta.

Da take bada shaida a kan lamarin daya daga cikin makwabtan Pistorius ta ce taji ihun mace tana neman taimako da tsakar dare daga bisani sai taji ihun namiji, kafin a karshe taji ihun mace inda kuma taji harbin bindiga har sau hudu. Sai dai Pistorius yace ya amince ya kashe ta amma ba da niyar kisan gilla ba a bisa kuskure ne haka kuma ya musanta sauran tuhumomin da ake masa da suka hadar da budewa wata mota wuta da yin harbi a wani wurin cin abinci da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

A ranar 14 ga watan Fabirerun shekarar da ta gabata ta 2013 ne dai Pistorius ya kashe budurwar tasa Reeva Steenkamp bayan sun dan samu sabani sa'oi kalilan kafin wannan lokaci da ake bikin ranar masoya ta Valentine.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe