1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ingantuwar rayuwar tsoffin mayakan tawaye

March 16, 2020

A shekara ta 2002 bayan fiye da shekaru 20 ana yaki tsakanin dakarun gwamnatin Yuganda da 'yan tawayen yankin yammacin Nile an amince da tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/3ZWl3
Rebellen in Südsudan
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

A kan babban titin birnin Yumbe shaguna da wuraren sayar da abinci suna hada-hada. Mazaunin birnin kimanin mutane dubu-50 suna walwala a shagunan cin cin abincin garin da ke yancin arewa maso yammacin kasar Yuganda, inda yake kuma samun masu ziyara. Akwai alamu kalilan da suka rage da ke tuna yakin basasa da ya faru.

Wannan ya faro lokacin da dakarun kasar Tanzaniya suka taimaka wa kungiyar 'yan twayen Yuganda da ke kasashen ketere kawo karshen gwamnatin kama karya ta Marigayi Idi Amin Dada a shekarar 1979. Dan kama karyan ya tsere zuwa kasra Libiya daga bisani zuwa Saudiyya.

'Yan gwagwarmayan sun musguna wa mutanen yankin bisa zargin goyon bayan Idi Amin Dada inda da yawa daga ciki suke tsere zuwa gudun hijira a yankin da yanzu ya zama kasar Sudan ta Kudu. Lamarin da ya tisla wa mutane suka dauki makamai, kuma yanzu shekara 18 da yarjejejiyar zaman lafiya da gwamnatin Yuganda. Waiga Rashid yana cikin yaran da suka dauki mukamai a wancan lokkaci:

Rebellen in Südsudan
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

"Bayan yarjejeniyar zaman lafiya wane kalubalen shi ne yafewa ko al'uma tana bukatar shirin yafe wa kowa, saboda al'uma an gaya mata cewa ta yafe."

An dauki matakin na yafe wa juna inda mayakan suka koma kauyukan da suka fito suka fara sabuwar rayuwa. Galibin manyan mutane da suka shiga tawayen suka janyo hankali wadanda suka zama mayakan 'yan tawaye. Ismael Maua yana cikin wadanda suka samu mukamai cikin mayakan 'yan tawayen gabanin samun zaman lafiya a kasar ta Yuganda:

"Yanayin duniyar ya tilasta mutun shiga wannan aikin. Yanayin duniyar yana sauyawa anan da can, abin da ya tilasta mun shiga daji."

Sannan Ismael Maua ya kara da cewa yanzu mutane suna rayuwa da sake sajewa domin yanayin rikicin ya sauya da kawo karshe. Mayakan 'yan tawayen na yankin arewa maso yammacin kasar Yuganda baya ga ahuwa, sun kuma samun karin tallafi a matakin sake sajewa da jama'a gami da taimakon kudade har da matsayi a rundunar soja da gwamnatin kasar. sai dai kauyawan ynakin sun tashi hannu rabbana, saboda sun amince da matakin yin ahuwa wa juna.

Rebellen in Südsudan
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Sai dai tsaffin mayakan sun yi maraba da wannan tsari na zaman lafiya da suka runguma a cewar Noah Achikule wanda ya yi nasarar gini rayuwa a matsayinsa na tsowon malamin makaranta:

"Har ta matata da yarana za su ba ni wani sabon abin yi, yadda mahaifi ke rayuwa, yadda zan yi kudanya da mutane. Zan yi haka domin su."

Yanzu dai tun bayan yarjejeniyar zaman lafiyar mutanen yankin arewa maso yammacin kasar Yuganda sun nutsuwa da koma harkokin rayuwa yau da kullum cikin tsanaki da kwanciyar hankali.