1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Scholz ya zama shugaban gwamnatin Jamus

December 8, 2021

Olaf Scholz mai shekaru 63 ya sha rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar Jamus ta Bundestag. Ya zama shugaban gwamnati na tara bayan karshen yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/43zg7
Deutschland Bundestag | Vereidigung Olaf Scholz
Hoto: John MacDougall/AFP/Getty Images

A yau Laraba ne (08.12.2021) aka rantsar da Olaf Scholz a matsayin shugaban gwamnatin Jamus, Inda ya maye gurbin Angela Merkel da ta kwashe shekaru 16 kan karagar mulki. Scholz mai shekaru 63 ya sha rantsuwar kama aiki ne a gaban majalisar dokokin kasar ta Bundestag. Scholz dai ya kasance shugaban gwamnati na tara bayan yakin dunya na biyu.

Sabon shugaban dai zai bude sabon babin gwamnati a kasar da ta fi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a nahiyar Turai, ko da yake ya sha alwashin dorawa daga inda tsohuwar shugaba Merkel ta dasa aya.

Tuni dai shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai Ursula von der Leyen da kuma shugaban majalisar EU Charles Michel suka aika da sakon murnarsu ga sabon shugaban gwammnatin na Jamus tare da alkawarin yin aiki tare. Shi ma a nashi sakon, shugaban kasar Chaina, Xi Jinping ya taya Scholz murna, ya na mai cewa Beijing zata yi aiki da shi don inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a sabon mataki.