1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Seleka da Anti-Balaka, na zargin junan su

August 6, 2014

Kungiyoyin biyu sun fara zargin juna a yankin arewa maso gabacin Afirka ta Tsakiya kan batun taka dokar tsagaita wuta da aka cimma a birnin Brazzaville.

https://p.dw.com/p/1CpiM
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Tsoffin 'yan tawayan Seleka da mayakan Anti-Balaka, na zargin juna da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka rattaba wa hannu a watan da ya gabata, bayan da aka shafe watanni da dama ana arangama a yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

'Yan kungiyar Seleka ne dai suka fara zargin 'yan Anti-Balaka da kai jerin hare-hare a yankin dake kalkashin kulawar su, bayan yarjejeniyar da aka rattabawa hannu ta ran 24 ga watan Yuli da ya gabata a Brazzavile babban birnin kasar Kongo.

A cewar Ahmat Nedjad, wannan yarjejeniya an take ta ne tun lokacin da akayi ta, inda aka kaiwa Musulmi hari a garuruwan Deokoa, Bodo, da Batangafo a karshen watan Yuli, har ma aka samu rasuwar sojoji guda biyu, na Tarayyar Afirka na Misca.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu