1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Seleka ta ki amincewa da sabuwar Firaminista

August 11, 2014

Kungiyar 'yan tawayen Seleka tace bata amince da sabuwar firaministaba kasancewar ba a tuntubesuba kafin zabin nata.

https://p.dw.com/p/1Csi9
Zentralafrikanische Republik Seleka Rebellen
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

'Yan tawayen Seleka na arewacin jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun yi fatali da yunkurin kafa gwamnatin hadaka, kasancewar ba a tuntubesuba kafin zabin sabuwar firaministar, abin da suke cewa zai sa su sake nazarin yarjejeniyar tsagaita wuta da suka kulla a watan da ya gabata.

Shugaba mai ci Catherine Samba Panza ta bayyana Mahamat Kamoun a matsayin wanda aka dora wa alhakin kafa gwamnati da zata samu karbuwar jama'ar kasar, ta kuma kai kasar ga gudanar da sabon zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa. Wannan dai na daga cikin irin matakan da gwamnatocin ke bi wajen kawo karshen kisan gilla da ake yi a wannan kasa da ya yi sanadin mutuwar dubban jama'a da sanya kimanin mutane miliyan daya kauracewa muhallansu.

Kamoun masanin tattalin arziki, ya kasance jagoran majalisar zartarwar kasar a lokacin gwamantin Micheal Djotodia, amma 'yan tawayen sun bayyana cewa ba mamba ba ne na kungiyar Seleka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba.