1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shakkun a Borno kan murkushe Boko Haram

January 9, 2017

Sabbin hare-hare da mayakan Boko Haram suka kai a jihohin Borno da Yobe da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 20 ya fara haifar da ayar tambaya kan ko da gaske ne an gama da 'yan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/2VWmQ
Karikatur: Nigeria - Armee erobert Boko Haram Hochburg Sambisa
Hoto: DW


A ranar Lahadi (08.01.2016)  wasu mata 'yan kunar bakin wake da ake zaton 'yan Kungiyar Boko Haram ne sun kai jerin hare-hare a sassan birnin Maiduguri inda suka halaka mutane da dama. Sannan kuma rundunar 'yan sanda ta jihar Borno ta sanar wa manaima labarai cewa wasu 'yan  kunar bakin wake guda uku dauke da bindigogi sun kutsa tashar mota ta Muna da ke hanyar Gambourun Ngala inda suka bude wutar suka kashe kutum daya kafin jami'an tsaro su harbesu. Sai kuma unguwar Kaleri da yankin Gwange inda wasu mata biyu suka kai harin kunar baki wake tare da halaka mutane biyu.


A cewar Injiniya Satomi Ahmad shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno wanda ya tabbatar da hare-haren ya ce karshen Boko Haram ne ya zo, shi ya sa ake samun sabbin salo na kai hare-hare. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka kai wasu hare-haren a ranakun Jumma'a da Asabar inda a Gubio a jihar ranar Jumma'a da yammaci 'yan Boko Haram suka auka wa wasu mutane yayin da suke kamun fara inda suka halaka 15 daga cikinsu.


Ranar Asabar da dare kuma wasu mayaka da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari kan wani barikin Sojoji a Buni Yadi a jihar Borno inda aka halaka wani jami'in Soja da kuma wasu kananan Sojoji biyar. Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da hare-haren sai dai bata bada karin bayani ba. Akwai barazanar irin wadannan hare-haren bama-bamai da shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ke fama da shi abinda ya sa mutane ke tambayar shin ko an gama da Kungiyar Boko Haram kuwa?

Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ce kai hari na kunar bakin wake alama ce ta karshen Boko Haram.Sai dai mazuana wasu yankuna kamar Buni Yadi sun bayyana cewa suna zargin akwai daruruwan mayakan Boko Haram a dazukan yankunansu. Saboda haka suka ce ya zama dole hukumomi su dauki matakai in ba haka ba rayuwarsu na cikin hadari.

Boko Haram
'Yan Boko Haram suka ce suna kan bakarsuHoto: Java