1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharadin Boko Haram na sakin matan Chibok

May 12, 2014

Shugaban kungiyar nan ta Boko Haram Abubakar Shekau ya ce a shirye kungiyarsu ta ke da ta saki 'yan matan nan na Chibok in gwamnatin Najeriya za ta saki mayakansu.

https://p.dw.com/p/1ByNR
Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau
Hoto: AP

A cikin wani sabon faifan bidiyo da ta kungiyar ta fidda a wannan Litinin din, Boko Haram din ta nuna 'yan matan na Chibok sanye da hijabai bakake da ruwan toka a zazzaune, har ma a wasu lokuta suka yi karatun kur'ani.

Kungiyar dai ta ce yanzu haka 'yan matan sun koma bin tafarkin addinin Islama domin kuwa sun karbi kalmar Shahada. A hirar da aka yi da wasunsu a bidiyon dai, guda daga cikin 'yan matan ta ce ba a cutar da su ba.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta ce komai ba game da wannan sabon bidiyon da Boko Haram din ta fidda, musamman ma dai irin bukatar da ta gabatarwa gwamnatin na sakin mayakansu kafin ta kai ga sakin 'yan matan na Chibok.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe