1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharadin Rasha game da taron kan Ukraine

May 6, 2014

Rasha ta ce dole ne a sanya 'yan aware a sahun wadanda za su halarci taron tattauna rikicin Ukraine da zai gudana a Geneva idan ana so a gano bakin zare warwareshi.

https://p.dw.com/p/1BulF
Hoto: Reuters

Kasar Rasha ta ce a shirya ta ke ta shiga a dama da ita a taron da zai tattauna makomar kasar Ukraine da za a gudanar a Geneva idan aka cika sharadin da ta gindaya. Ministan harkokin wajenta Serguei Lavrov ya ce sai idan an amince 'yan adawan Ukraine sun zauna kan teburin tattaunawa ne kwalliya za ta iya mayar da kudin sabulu. Shi dai lavrov da kuma takwaran aikinsa na Ukriane Andreii Deschtschiza suna halartar taron shekara- shekara na EU a Vienna inda suka gana bisa jagorancin ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier.

Sai dai kuma a daya hannun majalisar dokokin Ukraine ta yi watsi da duk wani yunkuri na gudanar da zaben raba gardama domin bai ma wani yankin na kasar damar samun kwarya-kwaryar cin gashin kansa. Yayin zaman da majalisar ta gudanar cikin sirri, wakilai 154 daga cikin 226 da majalisar da ta kunsa ne suka kada kuri'ar kin amincewa da batun na kuri'ar raba gardama.

Masu rajin ballewa na ta tayar da kayar baya a gabashin Ukraine da nufin dara kasar gida ta hanyar ba su damar zabar wa kansu makoma tsakanin Ukraine da kuma Rasha.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal