1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Jam'iyyar AFD na kara samun karbuwa a Jamus

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
September 2, 2019

Ranar daya ga watan Satumba ba wai rana ce ta tarihi kadai ba, rana ce da jam'iyyar masu tsantsar ra'ayin kishin kasa da kyamar baki ta AfD a Jamus ta samu sakamakon zabe da ya kara mata karfi a yankin gabashin Jamus.

https://p.dw.com/p/3OsuP
Berliner Runde ARD-Hauptstadtstudio Talkrunde LTW19 Landtagswahlen Sachen und Brandenburg
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Riedl

 

Ines Pohl ta fara sharhin ne da cewa, a ranar daya ga watan Satumba na shekara ta 1939 Jamus ta fara kai hare-hare a kan kasar Poland, abin da ya haddasa barkewar yakin duniya na biyu. An hallaka miliyoyin mutane tare da raunata wasu da dama, kana an ci zarafin mata baya ga dubban da aka tilasta wa kaurace wa gidaje da ma kasashensu, har yanzu duniya ba ta gama murmurewa daga masifar da 'yan Nazi suka sanya ta ba. Shekaru 80 cif bayan fara yakin duniya na biyun,

Ines Pohl babbar Editar tashar DW wacce ta rubuta sharhin wanda Lateefa Mustapha Ja'afar ta fasara
Ines Pohl babbar Editar tashar DW wacce ta rubuta sharhin wanda Lateefa Mustapha Ja'afar ta fasaraHoto: DW/P. Böll

wata jam'iyya a Jamus na murnar samun nasara, jam'iyyar da ke da tunani na tsantsar ra'ayin kishin kasa da kuma kyamar baki. A Jihohin Saxony da Brandenburg, sakamakon zaben da aka yi ya nunar da cewar AfD na kara samun tagomashi. Jam'iyyar da ta samu gagarumar nasara cikin shekaru kalilan a jihohin gabashin Jamus din biyu, inda ta mike daga karamar jam'iyya zuwa jam'iyyar siyasa ta biyu mafi karfi a majalisun dokokin jihohin. Ba abin mamaki ba ne, nan gaba jam'iyyar ta masu tsantsar kishin kasa ta zama jam'iyya mafi girma a Jihar Saxony.