1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Kalubale bayan hadewar Jamus

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
October 3, 2017

Bayan zaben Jamus, kasar na bikin sake hadewa lokacin da take neman kafa sabuwar gwamnati. Dole kasar ta tabbatar da cewa ta dauki matsayi a duniya, kamar yadda Ines Pohl babbar edita ta wannan tasha ta DW ta rubuta.

https://p.dw.com/p/2l9bV
Tag der Deutschen Einheit in Mainz
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

Tun shekarar 1990 kasar Jamus take bikin ranar 3 ga watan Oktoban kowace shekara game da sake hadewar kasar tsakanin sassan Yamma da Gabashi, inda ranar take zama a matsayin ranar hutu. Duk da rashin warware matsaloli masu sarkakiya, da rashin samun abin da ake tsammani, gami da rashin kammala wasu ayyuka, ranar ta zama wadda ake alfahari da ita. Ranar da duniya ta saka ido domin ganin ta kasance, an samu faduwar katangar Berlin cikin kwanciyar hankali duk da tsoron da ake da shi, tare da sake hadewar kasar Jamus wadda take karkashin tafarkin demokaradiyya da karfin tattalin arzikin da ke cikin jiga-jigai na duniya.

Amma zaben majalisar dokokin Bundestag na wannan shekara ta 2017 ya bar baya da kura, domin jam'iyyar AfD mai kyamar baki ta samu nasarar kashi 13 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda ta zama jam'iyya siyasa ta uku mafi karfi a Jamus. Tun lokacin ake samun korafi daga masu neman tabbatar da 'yanci da walwala, mutane suka tashi tsaye misali a shekarar 1989 a birnin Dresden domin tantance makomarsu inda suka ce "Mu ne mutane" kuma da haka suka tabbatar da ganin karshen rashin adalci na gwamnatin Gabashin Jamus ta wancan lokaci.

Ines Pohl Kommentarbild App
Babbar edita Ines Pohl ce ta rubuta sharhi kan hadewar JamusHoto: DW/P. Böll

Yanzu haka a karon farko jam'iyyar AfD ta shiga majalisar dokoki ta Bundestag domin haka labarin ya sauya. Cewar "Mu ne mutane" ba ya daga cikin abin da ya mamaye zance demokaradiyya. Sakon haka a garemu shi ne ba a maraba da 'yan gudun hijira wadanda suka shiga kasar Jamus a tsukin shekaru biyu da suka gabata. Sannan haka na nuna juya baya ga abin da ke faruwa a duniya.

Miliyoyin mutane suka tsere daga gidajensu sakamakon yake-yake, da bala'o'i, da fari ko kuma ambaliyar ruwa. Kana wasu milyoyin za su tsere nan gaba. Ba za a kawar da kai ba, za su shiga domin ganin an dama da su a harkokin rayuwa. Wadannan mutane ba dole ne ace suna neman zuwa kasashen Turai ba. Amma halin da suke ciki zai shafi sha'anin duniya baki daya.

Shi ya saka wannan taken na cewa "Mu ne mutane" bai tsaya ga 'yan siyasa kadai ba, har ya kai ga sauran kashi 87 cikin 100 na masu zaben Jamus wadanda suka kada kuri'un ga sauran jam'iyyu domin nuna rashin yarda da manufofin jam'iyyar AfD mai kyarmar baki. Ba kamar shekarar 1989 ba a wannan karo babu gamgami game da wannan kalma ta "mutane".

Nasarar jam'iyyar AfD a wasu sassan Yammacin Jamus ta kawar da tunani mai sauki game da rarrabuwar da ke tsakanin Yammaci da Gabashi. Yanzu tambayar ita ce tabbatar da kasar Jamus mai yalwa cikin kasashen Tarayyar Turai karkashin dokokin kasa bisa samun bunkasa. Wannan biki na 2017 game da sake hadewar Jamus ya zama na tasbihi.