1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHARHI KAN ZIYARAR DA SHUGABAN GWAMNATIN JAMUS, GERHARD SCHRÖDER, YA KAI A AFIRKA.

Yahaya Ahmed.January 26, 2004
https://p.dw.com/p/BvmL
Ziyarar da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard Schröder ya kai a Habasha, da Kenya, da Afirka Ta Kudu da Ghana a cikin makon da ya gabata dai, za ta iya kasancewa wata alama da ke nuna yadda Jamus ke daukar nahiyar Afirkan da muhimmanci. Amma duk da hakan, wasu masharhanta a nan kasar na ganin cewa, gwamnatin hadin gwiwa ta jam'iyyun SPD da Greens ta nan Jamus, ta yi jinkiri kwarai wajen tura shugabanta kai wannan ziyarar, musamman ma dai idan aka yi la'akari da cewar, sai da ta shafe shekaru dai-dai har biyar kan karagar mulki, kafin ta tuna da cewar, akwai wata nahiya makwabciyarta wadda ke da muhimmanci kwarai ga manufofin siyasar ketare ta Jumhuriyar Tarayyar Jamus, ko wane ne kuma ke jan ragamar mulkinta.
A halin yanzu dai, ba a san sakamakon da ziyarar ta Schröder zai janyo wa Afirkan da Jamus ba tukuna. Kome ake ciki dai, sai an jira a ga irin rawar da kungiyar nan ta sabunta yunkurin raya nahiyar Afirkan, wadda aka fi sani da suna NEPAD a takaice, za ta taka nan gaba. Nasarar da za a samu dai, za ta dogara ne kan yadda kasashen Afirkan da kansu za su iya bai wa juna shawara, su yi watsi da tafarkin nan na zaman `yan ba ruwanmu da abin da ke wakana a sauran kasashe makwabta, muddin lamarin bai shafe su ba. Kamata ya yi kuma, a sami wata kafa wadda za ta dinga lura da duk illolin da ke aukuwa a kasashen nahiyar, ta kuma yi gangami game da duk wata keta hakkin dan Adam da za ta ga ana yi a wata kasa ta nahiyar. Ta hakan ne dai za a iya cim ma halin tafiyad da mulki na adalci da kuma zaman lumana a duk kasashen Afirkan. Babban gwaji ga kasashen Afirkan a halin yanzu dai, shi ne yadda za su iya yin katsalandan don warware rikicin da gwamnatin shugaba Mugabe ke ciki a kasar Zimbabwe.
Afirka dai, har ila yau tana nesa da iya tsayawa da kanta wajen warware duk matsalolin siyasa da na tattalin arzikin da take huskanta. Sabili da haka ne kuwa take bukatan taimako daga ketare don iya shawo kan wadannan matsalolin a hankali. A nan dai, Jamus tana da muhimmiyar rawar takawa, wajen tallafa wa kafofin da ake da su a hannu yanzu, don cim ma gurin tabbatad da tsari na dimukradiyya mai dorewa a nahiyar. Sai dai kamata ya yi kowa ya san cewa, ba za a iya shawo kan duk matsalolin Afirkan a cikin dan gajeren lokaci ba. Kazalika kuma ya kamata kasashen Turai, su nuna hakuri ga yadda ababa ke wakana a nahiyar. Ba za a iya aiwatad da duk manufofin da aka tsara a Afirkan cikin gaggawa, kamar yadda aka saba da shi a Turai ba. Wani abin kuskure da kasashen Turan ke yi kuma, shi ne sa ran da su ke yi wajen ganin cewa, kome ya tafi daidai kamar yadda suke zato.
Duk da yabon ci gaba a mulkin dimukradiyya da kasashen Turan ke yi wa wasu kasashen Afirka, ba haka abin yake a zahiri a cikin kasashen da kansu ba. A lal misali, a kasar Kenya, wadda Jamus ta fi ba da misali da ita kamar kasar da ta yi nisa, a tafarkin dimukradiyya a nahiyar ta Afirka, har ila yau al'umman kasar na ta jira su ga wasu alamun sauyi na alkawarin da shugaba Mwai Kibaki ya dauka lokacin yakin neman zabensa. Bayan shekara daya da hawar karagar mulkin kasar, babu wani abin a zo a ganin da mafi yawan al'umman Kenyan za su iya jibinta shi da gwamnatin shugaba Kibaki. A Habasha ma, har ila yau gwamnatin kasar ba ta da kyakyawar suna a huskar kare hakkin dan Adam da kuma `yancin maneman labarai.
To a yanzu me za a iya cewa shugaban gwamnatin Jamus ya cim ma, a ziyarar da ya kai a Afirka k. A ko'ina dai shugaban ya yi ta nanata manufar siyasar Jamus a nahiyar, wadda kuma ta fi ba da karfi ga harkokin tsaro da na kiyaye zaman lafiya.
Amma ba wannan kawai ne nahiyar ke bukata ba. Babu shakka, Afirka ta fi bukatar a nuna mata zumunci a zahiri a yunkurin da take yi na fama da dimbin yawan matsalolin da take huskanta kamarsu bala'in fari da yunwa, da yake-yake, da gurbacewar yanayi da ambaliyar `yan gudun hijira. A nan kuwa, irin gudummuwar da kasashen Turai za su iya bayarwa shi ne yafe musu basussukan da suke binsu ba tare da sanya musu wasu sharudda ba, su kuma bude musu kofofin kasuwanninsu, don su iya shigowa da kayayyakin albarkatun noman da Allah ya sawwake musu.
Amma kafin a cim ma wani gagarumin nasara, sai duk kasashen Turan sun kirkiro sabuwar manufar siyasa ta bai daya, wadda dukkansu za su dinga bi. Ta hakan ne za a sami ci gaba, idan dai da gaske kasashen Turan suke, a kururuwar da suke yi na tausayawa wa al'umman nahiyar Afirka game da dimbin yawan matsalolin da suke huskanta.