1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Kone tutar wata kasa a Jamus wuce gona da iri ne

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
December 13, 2017

Jamus budaddiyar kasa ce mai kuma hakuri. Amma duk mai son yin rayuwa a Jamus dole ya girmama dokokin kasar, ciki har da yaki da masu kyamar Yahudawa inji babbar editar DW Ines Pohl.

https://p.dw.com/p/2pIUZ
Deutschland Demonstranten verbrennen Fahne mit Davidstern in Berlin
Hoto: picture alliance/dpa/Jüdisches Forum für Demokratie und gegen Antisemitismus e.V.

Ines Polh ta ce 'yancin yin zanga-zanga na da babbar kariya a Jamus. A kan iya takaita shi ne kawai a cikin wani yanayi na tabbatar da tsaro. Alla-kulli-hali dai za a iya cewar a yau demokaradiyya na fuskantar kalubale a Jamus ta yadda a karo da dama a kan titunan a kan samu masu bayyana kalamun da suka saba wa demokaradiyya a lokacin gangami. Al misali furta kalamun cewar baki su yi waje su bar kasar.

Jamus dai  ta karantu cikin nadama da irin munanan abubuwa da suka faru a baya na 'yan mulkin kama karya na 'yan Nazi lokacin da gwamnati ke iya haramta gangami kan hanya don hana jama'a bayyana ra'ayoyinsu.

To amma yanzu ga yanayi da ake ciki za a iya ganin gwamnatin Angela Merkel na shan suka,  abu ne da akan iya samu, haka ma 'yan Falasdinu da ke zaune a nan Jamus na iya yin zanga-zangarsu a gaban ofishin jakadancin Amirka domin nuna bacin ransu sakamakon matakin da Amirka ta dauka a kan Birnin Kudus amma cikin ka'ida kamar yadda dokokin Jamus suka tanada.

Bai kamata Jamus ta kau da kai ba

Ines Polh ta ce tarihin da muke da shi ya hana mu wuce gona da iri, kuma ba komai za mu iya bari a yi ba. Ko da shi ke ma a baya Jamus ta yi sanadin mutuwar Yahudawa miliyan shida. Kuma Jamus na da babban nauyi a kanta na yaki da nuna wa Yahudawa wariya.

Ines Pohl Kommentarbild App
Ines Pohl babbar editar tashar DWHoto: DW/P. Böll

Don haka ba za a taba amincewa ba da kone tuta har ma da shaidar tutar Yahudawa a Jamus. Masu neman kariya da neman mafaka a Jamus dole su dukkaninsu su ba da hadin kai ga fafutukar da kasar ke yi na yaki da nuna wa Yahudawa wariya.

Jamus kasar 'yan ci-rani

A wasu kasashen a kan iya kone tuta domin tozarta makiyi, amma kundin tsarin mulkin Jamus ya ta'allaka ne a kan mutunta wasu da kuma ba da kariya ga tsiraru. Ko da shi ke ma ta fannin shari'a ba lalle ba ne hakan ya zama wajibi. Ba mai dai sai tutar Isra'ila ba, gaba daya ba za a taba amincewa ba da kona tuta ko ta Turkiyya ko Rasha ko Amirka ko Saudiyya duk da irin halin da gwamnatocin ke shan suka.

Don haka mu yi rayuwa tare a cikin kasar da ke karbar baki wato Jamus a cewar Ines Polh. Ta ce hakan ba zai taba yiwuwa ba sai muna tunani da tarihinmun, don kasancewa cikin makoma ta gari, kuma wadanda ba su bada goyon baya ga abin da muka gada na tarihi ba za su iya samun makoma ba a nan. Wannan kuwa babu tantama ko jayaya a cikinsa.