1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Dambarwa kan 'yan gudun hijira

Kroll Katharina Kommentarbild App
Katharina Kroll
June 19, 2018

A cewar marubuciyar sharhi Katharina Kroll, da kamar wuya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta cimma warware matsaloli kan 'yan gudun hijira da takwarorinta na Turai.

https://p.dw.com/p/2zrOX
Trump Merkel
Merkel na fuskantar tsaiko kan amsar 'yan gudun hijraHoto: Picture alliance/AP Photo/M. Schreiber

Angela Merkel ta waiwayi kasashen Turai a daidai lokacin da ruwa ke neman kare wa dan Kada a dangane da takaddamar karbar 'yan ci rani. Ya zama wajibi a gareta ta hada kai da sauran takwarorinta na Turai domin cimma matsayar bai daya kan manufofin 'yan gudun hijirar, lamarin da zai burge jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta CSU da ta gallabeta a kan wannan batu. In ba haka ba, ministan harkokin cikin gida na Tarayya Horst Seehofer ya yi barazanar rufe iyakar Jamus ga 'yan gudun hijira.

Jam'iyyar CSU ta bai wa Merkel lokaci don daukan mataki ko kuma ta yi ta gabanta ta hanyar maida 'yan gudun hijira da aka musu rajista a wasu ƙasashen Turai, lamarin da zai karkata akalar matsalar zuwa wasu kasashen Turai, ma'ana za a gudu ba tsira ba. Shekaru uku Angela Merkel ta shafe tana kokarin warware matsalar 'yan gudun hijira a kungiyar EU amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Saboda haka cikin wa‘adin kwanaki 14 da ta dibar wa kanta, da kamar wuya ta samu nasara. Amma kuma ba ta da zabi saboda rikicin 'yan gudun hijirar na barazana ga abin da ya danganci manufofin siyasa ta. Sannan yanzu ba Jamus kadai ruwan rikicin zai ci ba, amma yana barazana ga hadin kan Turai.

Kroll Katharina Kommentarbild App
Katharina Kroll, marubuciyar sharhi a DW

Dole ne Shugabar gwamnatin Jamus ta tabbatar da cewa kungiyar Tarayyar Turai ba ta ruguje ba, kuma Jamus ta iya zama mai karfin iko a wannan "Duniya da ke cikin hargitsi," Ko da Merkel sai da ta nuna muhimmanci hada karfi da karfe tsakanin kasashen Turai kan batun na 'yan gudun hijra a ranar Asabar da ta gabata.

Yanzu dai makomar siyasar Angela Merkel na hannun wasu gwamnatocin Turai ciki har da kasar Girka da Italiya da Ostiryia, wadannan take son cimma yarjejeniyar da su don su karbi ‘yan gudun hijirar da suka zo daga Jamus. Ita dai jam'iyyar CSU da ke kawance da CDU ba wa Merkel wa'adin warware rikicin. Abinda ke zama alamar shan suka kan batun a gamayyar jam'iyyun da ke mulki da ke barazanar rushe kawancen.

A taron manema labarai da ta gudanar, Angela Merkel ta yi kokarin  bayyana matsayi daban-daban, inda ta yi fatali da wa'adin ministan cikin gida ko da ba a samu ci gaba ba a tattaunawar da za ta yi da kasashen Turai ba. Tabbas a matsayinta na shugabar gwamnanati tana ikon. A dayan hannu kuma ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofer ya yi fatan shugabar gwamnati ta yi nasara. Amma kuma ya fito karara ya bayyana cewar zai aiwatar da manufofin da ya sa gaba kan 'yan gudun hijira idan Angela Merkel ta kasa dawo da sakamako na gari daga birnin Brussels. Wannan tufka da warwara da jam'iyyar jihar Bayern ke yi na barazanar ga jerawa da jam'iyyar CDU ta Merkel da CSU ta Seehofer suka dade suka yi tare don su tsira tare.