1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Assad da gazawar kasashen yamma

July 17, 2020

A wannan Jumma'a Shugaba Bashar al-Assad na Siriya ya cika shekaru 20 a kan karagar mulkin kasar. Duk da yakin da ake ci gaba da gwabzawa a kasarsa, shugaban na kan madafun iko daram. Godiya ga tallafin Rasha da Iran.

https://p.dw.com/p/3fVjD
Syrien Bashar Al-Assad 1999
Shugaba Bashar Al-Assad na SiriyaHoto: Getty Images/AFP/R. Moghrabi

Cikin sharhin da ya rubuta, Rainer Solich na tashar DW  ya nunar da cewa shekaru 20 ke nan Bashar al-Assad na shugabanci a kasar Siriya, kuma bisa ra'ayinsa ya aiwatar da abubuwa masu gamsarwa. Da karfin hatsi ya murkushe bore na yunkurin kawo karshen mulkinsa a shekarar 2011, lokacin da guguwar sauyi ta kada a kasashen Larabawa, sannan ya yi galaba a yakin da ya biyo baya saboda taimakon sojoji da makamai daga kasashen Rasha da Iran. Yanzu masu adawa da Assad na iko ne da wasu yankuna kalilan, sun kuma koma wani kawancen 'yan tarzoma na addini da ba su da tasiri.

Gara Asad da kungiyar IS

Ko da yake wadannan 'yan tarzoma na samun dan tallafi daga kasar Turkiyya, amma saboda ayyukan rashin imani na kungiyar IS da wasu kungiyoyi makamantanta, ya sa masu bibiyar al'amura daga kasashen yamma na ganin cewa Assad da ke zama dan mulkin kama karya ya dan fi imani, lamarin da ya sa tuni gwamnatocin yamma suka daina kira da ya yi murabus.

Sollich Rainer Kommentarbild App
Rainer Sollich na tashar DW

Su kuma 'yan adawa masu rajin mulkin dimukuradiyya a Siriya da a farko ke samun goyon bayan kasashen Turai da Amirka, yanzu an mayar da su saniyar ware. Wannan na zama wata nasara ga shugaban na Siriya. Kasancewar Assad har yanzu a kan karagar mulki, ba sakamakon katsalandan din Rasha da Iran ne kadai ba, gazawar kasashen yamma ma ta taka rawa.

Kasashen yamma sun kai 'yan Siriya sun baro.

Kasar Amirka karkashin Shugaba Donald Trump ta dukufa wajen janye sojojinta daga yankin, ta kuma fi mayar da hankali kan batutuwanta na cikin gida. Shi ma tsohon Shugaba Barack Obama na Amirkan, kusan ya mayar da manufofin kasashen yamma a Siriya, abin dariya ko ma karen da baya haushi, lokacin da ya yi barazanar daukar matakai kan Siriya matukar gwamnati ta yi amfani da makamai masu guba, sai dai babu abin da ya biyo bayan wannan barazana. Ita kuma kungiyar EU ta takaita aikin ga batun jin kai, sannan ta yi ta kokarin ganin ba a samu karuwar yawan 'yan gudun hijira daga Siriya da ma yankin Gabas ta Tsakiya zuwa Turai ba.

BG Flüchtlinge Idlib
Miliyoyin 'yan Siriya na gudun hijiraHoto: Getty Images/B. Kara

A nan dai Turkiyya da ke zama mamba da ba a mutunta wa sosai a kungiyar NATO, ta mayar da kanta mai tsaron iyakokin Turai yayin da ake cikin halin ni 'ya su a sansanonin 'yan gudun hijirar da ke kasar Girka da yanzu babu mai kula da su. Kasashen yamma sun kai 'yan Siriya sun baro.

Dole a binciki batun aikata laifin yaki

Motsi ya fi labewa inji masu iya magana. Yanzu haka a wassu kasashen EU kamar Jamus, an fara shari'ar wasu 'yan Siriya da ake zargi da aikata laifukan yaki, daga bangaren gwamnati da ma 'yan adawa masu ikirarin Jihadi. Shari'ar wadannan mutane na da muhimmanci kuma abin a yaba ne. Fata dai shi ne watan wata rana a gudanar da bincike a kan rawar da kasashen yankin Golf da Turkiyya suka taka wajen tallafa wa kungiyoyi masu daukar makamai.

Tabbas akwai babban alhaki a siyasance a kan wadanda ke da hannu a rayukan mutane kimanin dubu 500 da suka salwanta a yakin Siriya, da ruwan bama-baman da ake a kan fararen hula da makarantu da asibitoci. An san wadanda suka aikata wannan laifi, idan da gaske ake wajen yi wa al'umar Siriya adalci. Babban mai alifi shi ne mutumin da ya kwashe shekaru 20 a fadar shugaban kasa da ke birnin Damaskus, da mukarrabansa da ke a biranen Moscow da Tehran.