1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridu

Tijani LawalMarch 7, 2008

Sharhin Jaridun Jamus akan Afurka

https://p.dw.com/p/DKtc
Shugaban Kamaru,Paul BiyaHoto: AP Photo


Kamerun/Sudan/Kenya

A wannan makon dai mawuyacin halin da ake fama da shi a kasar Kamaru shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, inda zamu fara da duba sharhin jaridar Der Tagesspiegel dake cewar bayan Kenya da Chadi a yanzun kasar Kamaru, wadda ta taba zama karkashin mulkin mallakar Jamus, ita ce ke fuskantar barazanar durmuya cikin tashe-tashen hankula, inda akalla mutane 17 suka yi asarar rayukansu. Jaridar ta ce:

Kamerun

"Abin mamaki a game da wannan mummunan ci gaba da ake samu a Kamaru shi ne kasancewar shugaba Paul Biya na kasar, a maimakon ya nemi ainifin bakin zaren warware wannan rikici, sai shiga dora wa abokan hamayyarsa laifi. Yau fa kimanin shekaru 25 ke nan cir Paul Biya na mulki a wannan kasa, amma har yau bai fara tunanin ritaya ba. A yanzu haka shugaban kokari yake yi yayi wa kundin tsarin mulkin Kamaru kwaskwarima ta yadda zai samu ikon yin ta-zarce a shekara ta 2011 bayan ya samu shekaru 77 da haifuwa."

A cikin nata sharhin jaridar Neues Deutschland tayi nuni ne da cewar ba koma ba ne musabbabin wannan rikici illa tsadar rayuwa da kuma yunkurin shugaba Biya na aiwatar da canje-canje ga daftarin tsarin mulkin kasar Kamaru. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Ko da yake ga alamu kura ta lafa a tashe-tashen hankulan da kasar Kamaru ta fuskanta, amma fa a a hakika har yau tana kasa tana dabo dangane da fushin dake tattare a zukatan al'umar wannan kasa a game da shugabansu dake mulki tun daga shekara ta 1982. Wannan takaicin shi ne ya harzuka jama'a suka shiga ta da kayar baya a kasar ta Kamaru wadda ta fi kowace kasa a nahiyar Afurka fama da cin hanci."

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar matsalar ne daki-daki inda take cewar:

"Da farkon fari dai hauhawar farashin kayan masarufi, wadda a tsakanin watanni biyu kacal ta kai kashi 65%. Wannan hauhawar farashi kuwa bata da nasaba da rashin damina mai albarka. Babban ummal'aba'isinta shi ne tashin gwawron zabo da farashin danyyen mai yayi a kasuwannin duniya, kamar yadda kwararrun masana suke gani. Amma idan an sake bitar al'amuran Kamaru za a ga ta fi kowace kasa duniyar nan gaba daya fama da matsalar cin hanci, a yayinda shi kuma shugabanta a maimakon ya magance wa talakawa wannan matsala, sai nuna son kai yake yi yana mai neman yin ta-zarce."

Sudan

A halin yanzu rikicin Darfur ta kasar Sudan ya durfafi shekarunsa na shida, a yayinda a daya bangaren babu wata nasara ko da 'yar kankanuwa ce da za a iya cewar MDD ta cimma a fafutukar lafar da kurar wannan rikici, a cewar jaridar Der Tagespiegel, wadda ta kuma kara da cewar:


"Rikicin Darfur na daya daga cikin munanan rikice-rikicen da aka taba fuskanta kuma ya fi kowane jefa dimbin mutanen da ba su san hawa ba ba su san sauka ba cikin halin kaka-nika-yi a duk fadin duniya. A sakamakon haka aka tsayar da shawarar mayar da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD ya zama shi ne mafi girma da majalisar ta gabatar a cikin tarihinta, inda aka yi niyyar tura sojoji dubu 26 da zasu rufa wa sojojin Kungiyar Tarayyar Afurka dubu 7 da aka tsugunar a lardin na Darfur. Amma fa har yanzu kwalliya ba ta mayar da kudin sabulu a game da fatan da aka yi na lafar da kurar rikicin ba."

Kenya

A can kasar Kenya ga alamu haka ya cimma ruwa dangane da kokarin da tsofon sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya sha famar yi domin dinke barakar da ta biyo bayan zaben kasar da aka gudanar watan desamban da ya wuce a cewar jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta kara da cewar:


"Muhimmin abu a game da nasarar da Kofi Annan ya cimma a rikicin Kenya shi ne, akalla ya taimaka kasar ta samu 'yar sararawa, ko da kuwa daga bisani masu hannu a sulhun zasu sake bijire wa daidaituwar da aka samu tsakaninsu game da rabon madafun mulki. Mai yiwuwa wannan sararawar ta zama wani mataki na farko akan hanyar warkar da tabon da tashe-tashen hankulan kasar ya haifar tsakanin kabilunta."