1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Suleiman Babayo
July 10, 2020

Tasirin tsarin kiwon lafiya a Afirka da batun Ilmi da kuma jana'izar fitaccen mawakin nan na kasar Habasha da ya rasu Hachalu Hundessa sun dauki hankalin sharhin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3f7Uy
Äthiopien Beerdigung Haacaaluu Hundeessaa in Ambo
Hoto: Reuters/Oromia Broadcasting Network

Za mu dauko sharhin da Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta yi sharhi kan halin da ake ciki a kasar Habasha. Jaridar ta ce mawaki mai zanga-zanga Hachalu Hundessa ya samu Jana‘izar girmamawa da aka nuna kai tsaye a kafofin yada labaran gwamnati tare da maci na jami'an tsaro. An harbi mawakin Hachalu Hundessa a birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar ta Shabasha kuma daga bisani ya cika a babban asibiti. Lamarin da ya janyo bore ga gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed inda kimanin mutane 90 suka rasa rayukansu.

A sharhin Jaridar Die Zeit mai taken ko a harkar ilimi, ko tsarin kiwon lafiya, kasashen Afirka na kara bunkasa. Jaridar ta ba da misali da kasar Laberiya a shekara ta 2015 inda ministan ilimi na wancan lokacin George Werner ya tabbatar da nakasu ga tsarin ilimin kasar ta yammacin Afirka wadda ke sahun gaba a kasashe 'yan rabbana ka wadata mu. A lokacin dalibai 25,000 suka rubuta jarabar kammala babbar makaranta amma babu wanda ya yi nasarar cin jarabawar ta shiga jami'a. Jaridar ta ce matakan da aka dauka na tsarkake harkokin ilimin na samun nasara, wadanda suka hada da korar malaman jabu 2000 daga bakin aiki da kara horas da malamai. A gaba daya idan aka duba kama daga Afirka ta Kudu da aka bude makarantun mata masu juna biyu da kara samun shigar da yara makaranta a kasashen nahiyar akwai nasararorin da aka samu ta bangaren ilimi.

Liberia Monrovia 2013 | Studenten & Prüfung
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

A cikin sharhin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung bisa annobar coronavirus ya nuna irin hadarin da namun daji ke ciki na farauta ba bisa ka'ida ba. Wannan ya hada da katsewar kudin yawan bude ido da ke taimakawa wajen tafiyar da gandun daji, inda a kasar Malamai ga misali aka samu matukar raguwar wannan kudin. Raguwar masu yawan bude idon ya kai kashi 90 cikin 100 a wusu wuraren.

Ita ma jaridar Neues Deutschland a cikin sharhin mai taken annobar cutar coronavirus ta kassara nasarar neman kawar da yunwa a kasashen Afirka. Jaridar ta yi nuni da rahoton kungiyar yaki da yunwa ta duniya yayin da ake killace mutane a gida domin kare yaduwar annobar coronavirus a hannu daya fari sun far ma gonaki a kasashen gabashin Afirka. Abin da ya tabarbara lamura kama daga Habasha zuwa Kenya da Sudan. A kasar Kenya ga misali kashi 29 cikin 100 na mutane na cikin yunwa yayin da kimanin kashi 60 cikin 100 iyalai suna karkashin mizanin talauci.

Ghana Accra | Coronavirus | Chinesische Hilfsgüter
Hoto: imago images/X. Zheng

Ana ta bangaren jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi kan taimakon da manyan kasashe suka yi wa kasashen maso tasowa domin dakile annobar coronavirus. Shin haka ne kawai? Jaridar ta duba irin misali a Afirka ta Kudu haka kabura ya habaka sakamakon yawan masu dauke da wannan cuta. Ana sa ran kimanin mutane 9,000 za su mutu daga wannan cuta ta coronavirus a lardin Western Cape na Afirka ta Kudu kadai wanda ke dauke da mutane milyan shida. Yayin da Afirka ta Kudu ke kara karfafa gwajin cutar coronavirus a daya bangaren har yanzu a Najeriya ana jan kafa kan fadada gwajin. Manyan kasashen dai suna taka rawa wajen karfafa matakan yaki da annobar ta coronavirus a nahiyar Afirka.