1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru Awal AH
July 6, 2018

Yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar a makon da ya gabata ta dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/30xSp
Südsudan | Unterzeichnung Waffenstillstandsvereinbarung
Hoto: REUTERS

Jaridar ta ce ‘yan tawayen Sudan ta Kudu da gwamnatin kasar sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da ke da burin kawo karshen yakin basasa a kasar sai dai masharhanta na nuna shakku. Bayan tattaunawa da suka yi makon da ya gabata a Khartoum babban birnin kasar Sudan, sassan biyu karkashin shiga tsakani daga Shugaba Omar al-Bashir na Sudan da takwaransa na Yuganda Yoweri Museveni suka amince da sabon yunkurin na wanzar da zaman lafiya.  Amma ganin yadda a baya bangarorin da ke rikici a Sudan ta Kudun sun yi ta karya yarjeniyoyin zaman lafiya, a wannan karon ma ba za ta canja zane ba. Wani abin da ke gaskata wannan shakku shi ne, jim kadan bayan da yarjejeniyar ta fara aiki, dakarun gwamnati sun kai hari kan sansanonin ‘yan tawaye a garin Moboro da ke lardin Wau.

 kamfanin Volkswagen ya bude ma'aikatar hahada motoci a Kigali babban birnin kasar Ruwanda

Ruanda Volkswagen - Smartphone
Hoto: DW/S. Schlindwein

Sabbin harkokin kasuwanci a Afirka inji jaridar Neues Deutschland. Ta ce Afirka ba nahiya ce da ta rasa alkibla ba, kamar yadda rahotanni dangane da matsalar ‘yan gudun hijira ke nunawa. Jaridar ta ce a yankuna masu yawa na Afirka harkokin kasuwanci na bunkasa, su ma kamfanonin Jamus na cin gajiyar wannan ci gaban. Ko da yake nahiyar na fama da jerin kalubale, amma kuma tana da damarmaki da yawan gaske. A baya bayan nan kamfanin Jamus da ke kera motocin samfurin Volkswaja ya bude ma'aikatar harhada motoci a Kigali babban birnin kasar Ruwanda, inda a kowace shekara za a harhada motoci kimanin 5000 ga kasuwar cikin gida ta yankin gabashin Afirka. Yanzu haka dai an fara da samfurin Polo da Passat. Wasu kamfanonin Jamus sun bi sahu suna bude rassansu a nahiyar ta Afirka.

Soma aikin hako ma'adinai a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango bayan da gwamnatin ta ba da izini

Neues Bergbaugesetz in der RD Kongo
Hoto: Getty Images/AFP/S. Tounsi

Kwango ta ba da izinin aikin hakan rijiyoyin mai a yankin gandun daji da ke karkashin kariya, inji jaridar Die Tageszeitung, wadda ta kara da cewa gandun dajin da ke zama gida ga gwaggwan birai da wasu namun dawa, na fuskantar barazana. Za a rage girman gandun daji na Virunga da Salonga don ba da dama ga aikin hakar mai. Aikin na hadin gwiwa tsakanin kamfanin mai na Kwango da na Comiao mallakin wani dan kasar Afirka ta Kudu mai asali daga kasar Girika, zai samar wa kasar dala miliyan dubu bakwai a cewar gwamnatin Kwango. Wani kudurin majalisar dokoki ya amince da aikin wanda masu fafatukar kare muhalli suka ce ba a ba da la'akari da dokar kare muhalli ba wadda ta tanadi yin bincike mai zurfi kafin wani aiki a gandun daji da ke karkashin kariya da duba illar da aikin zai yi tare kuma da duba hakkin mazauna yankin.