1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar 'yan kungiyar Al-Kaida a Jamus

Mohammad Nasiru AwalNovember 13, 2014

Wata kotu a birnin Düsseldorf ta ynke wa wasu magoya bayan Al-Kaida hukunci daurin shekaru masu yawa a kurkuku.

https://p.dw.com/p/1Dmcj
Prozess gegen Al Kaida Mitglieder am Oberlandesgericht Düsseldorf 13.11.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Gambarini

A shari'ar da aka yi wa membobi hudu da kuma magoya bayan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Kaida, kotun kolin jiha ta birnin Düsseldorf da ke jihar nan ta North Rhein Westfalia ta yanke wa 'yan tarzomar hukuncin daurin shekaru hudu da rabi zuwa shekaru tara a kurkuku. Mutanen da ake wa lakabi da 'yan kungiyar Al-Kaida a birnin Düsseldorf, an same su da laifin kokarin shirya kai munanan hare-hare a Jamus bisa umarnin kungiyar Al-Kaida. A shekarar 2011 aka cafke mutanen kuma aka tsare su bisa zama 'ya'yan wata haramtacciyar kungiyar 'yan ta'adda ta ketare. An tuhume su da shirya harhada bama-bamai.