1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shari'un zabe sun isa kotun kolin Najeriya

September 22, 2023

A yayin da hankula ke karkata zuwa kotun koli a cikin neman mafitar rikicin zabukan Najeriya na shekarar bana, akwai dai tsoron kotun na shirin yanke hukunci cikin yanayi mai wahala.

https://p.dw.com/p/4WhYU
Najeriya | Kotu a birnin Abuja
Najeriya kotuHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Kotun dake zaman mafi tasiri da kuma daukaci na yan kasar ke kallon adalci a ciki. To sai dai kuma daga dukka na alamu, kotun tana shirin adalcin a cikin mawuyaci na hali da kila mamatsi  na lokaci. Ya zuwa yanzun dai akalla alkalai 10 cikin 21 dake cikin kotun dai ko sun yi ritaya ko kuma sun rasa ransu. A yayin kuma da dokar zabe ta kasar tace akalla alkalai bakwai cikin 11 da suka rage ne zasu saurari karraraki na zabe na shugaban kasar.

Najeriya I Tsarin zaman kotun Najeriya
Tsarin zaman kotun NajeriyaHoto: REUTERS

Ko bayan nan dai alkalai guda biyar ne suke shirin sauraron daukaka karar gwamnoni a zabukan jihohi 28. Kuma duk a cikin tsawon kwanaki 60 a wani abun dake iya kaiwa ya zuwa ga takura da kila  ma matsa lamba cikin gidan alkalan. Akwai dai tsoron yanke hukunci cikin matsi na lokaci da kila nuna alamun gajiya a bangaren alkalan dake da jan aikin kwantar d ahankulacikin gidan na siyasa d akila sauran jama'ar gari. Buba Galadima dai na zaman jigon jam'iyyar NNPP na kasa, kuma ya dauki lokaci yana fafutukar shari'ar ta siyasa a cikin Najeriya.

Kuskure cikin gidan alkalai, ko kuma  dama ta dadawa 'yan uwa da abokai dai, duk da karancin alkalan da lokaci cikin sabbin shari'un dai kwalliya tana iya kai wa ga wanke sabulu a fadar Barrister Mohammed Shu'aib da ke zaman wani lauyan da ke hada-hada a kotun kolin.

Zaben Najeriya | Peter Obi, da Bola Tinubu (tsakiya),da  Atiku Abubakar
Peter Obi, da Bola Tinubu (tsakiya),da Atiku Abubakar Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Juriya cikin hukuncin shari'a, sabon yanayin dai na zamna irin sa na farko cikin kasar a lokaci mai nisa. Kuma ko ta ina sabbabin mammalakan kasar ke shirin su bi da nufin kara yawan  alkalan a cikin kotun koli, akwai dai  tsoron matsi na lambar na iya shafar ingancin shari'u dakila ma makomar tsarin demukuradiyya na kasar da ke dogaro bisa kotun da nufin inganci. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batun na siyasa, kuma ya ce cukumurdin tsarin na jefa kasar cikin barazanar gaza samun shugabanci mai kyau. Abun jira a gani dai na zamna yadda take shirin kayawar a tsakanin alkalan da ke shirin yanke hukuncin.