1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekar 16 da kissar ƙare dangi a Ruwanda

April 7, 2010

Majalisa Ɗinkin Duniya ta aike da saƙon jaje don tunawa da kissar kiyashin Ruwanda

https://p.dw.com/p/Mpj6
Hoto: AP

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, ya sanar da cewar, kyakkyawar hanyar da al'ummar Duniya zata tuna da kissar ƙare dangin ƙasar Ruwanda a shekara ta 1994 ita ce, sabunta ƙudurin hana afkuwar irin ta'asar a nan gaba. A cikin wata sanarwar da ofishin kula da harkokin 'yan jaridun majalisar ya fitar game da cika shekaru 16 da yin kissar, Sakatare Janar ɗin ya ce, Duniya ta dunƙule wuri guda wajen yin yaƙi da kissar ƙare dangi, aikata manyan laifukan yaƙi, da kuma yin karan tsaye ga haƙƙin bil'adama da na ƙananan ƙabilu. Ban ya miƙa wannan saƙon ne a dai dai lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Vienna, bayan rangadin daya kai zuwa nahiyar Asiya. Kimanin mutane dubu 800 - galibinsu 'yan ƙabilar Tutsi ne suka mutu a kissar ƙare dangin, wadda 'yan ƙabilar Hutu - masu tsattsaurar ra'ayi suka tsara kuma suka aiwatar.

A zantawar da ta yi da tashar Deutsche Welle domin zagayowar ranar tunawa da kissar, jakadiyar ƙasar Ruwanda a Tanzania, Fatuma Ndagiza, wadda ta shugabanci hukumar sasanta tsakanin al'ummar ƙasar bayan matsalar, bayyana farin ciki ta yi game da ƙaunar junan dake tsakanin 'yan Ruwanda a yanzu:

" Muna farin cikin ɗaukar matakin daya kai ga bunƙasa haɗin kai da kuma yafewa juna. A yanzu waɗanda matsalar ta shafa, da kuma waɗanda ke da alhakin yin hakan, dukkansu na zaman lafiya da lumana, saboda afuwar da masu laifi suka nema, kuma aka yafe musu."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas