1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara daya a kan mulki, kwanaki hudu a Habasha

March 18, 2013

Ziyarar Joachim Gauck a Habasha ita ce ta farko da shugaban na Jamus ya kai nahiyar Afirka tun bayan darewarsa kan wannan mukami a bara.

https://p.dw.com/p/17zp2
Bundespräsident Joachim Gauck zu Besuch in Äthiopien. copyright: Hendrik Schott zugeliefert von: Lina Hoffmann
Hoto: DW/H. Schott

Shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauck ya yi kira ga kasashen Afirka da su bude wani sabon babi na demokradiyya da girmama doka. Shugaban na Jamus ya yi wannan kira ne a wani jawabi da ya yi a gaban wani taron kungiyar tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Gauck wanda a wannan Litinin ya cika shekara daya cur a kan kujerar shugabancin Jamus, yana wata ziyarar kwanaki hudu ne a kasar ta Habasha.

Joachim Gauck wanda wannan ita ce ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka tun bayan darewarsa karagar shugabancin Jamus a bara, ya fada wa taron kungiyar tarayyar Afirka cewa ya kamata a dukkan kasashen Afirka da ke da zababbiyar gwamnatin demokradiyya a karfafa ikon majalisun dokoki. Jawabin na sa a gaban taron kungiyar tarayyar Afirka na zama daya daga cikin muhimman batutuwan da za su mamaye ziyararsa ta yini hudu a Habasha, kuma ya fada wa shugabannin na Afirka da su tsaya tsayin daka a yaki da cin hanci da rashawa sannan su mutunta hakkin dan Adam da aiki da dokar kasa.

AU za ta sa kafar wando guda da masu fatali da tsarin mulki

"Duk shugaban da ya yi fatali da kundin tsarin mulki domin yin tazarce, duk wanda ya yi juyin mulki ya san cewa kungiyar tarayyar Afirka za ta zama abokiyar gabarsa."

Tun a ranar Lahadi Gauck mai shekaru 73 a duniya ya isa birnin Addis Ababa kuma ya ci abincin dare da Firaminista Hailemariam Desalegn. A wannan Litinin kuma ya gana da kungiyoyin farar hula kasar inda ya yaba da ayyukan da suke yi duk da tursasawa da suke fuskanta daga hukumomin kasar.

Gauck in Äthiopien
Hoto: DW/H. Schott

" Sun yi mini bayani inda matsalolin suke, mun tattauna game da hakkin dan Adam da yadda za a tabbatar da 'yancin mata da makiyaya da sauran mutanen da za su taka rawa wajen sake fasalta wannan al'uma."

Cin zarafin al'uma bai kau ba

Har yanzu kasar Habasha duk da sabon Firaminista Hailemariam Desalegn da ya gaji marigayi Meles Zenawi a bara, na amfani da wata dokar yaki da ta'adanci tana gallaza wa 'yan jarida masu zaman kansu da kuma 'yan adawa.

Thilo Hoppe dan majalisar dokokin Jamus kuma mukaddashin shugaban kwamitin majalisa mai kula da hadin kan tattalin arziki da raya kasa, ya ce shugaban na ziyara ne a wata kasa mai takaita 'yancin siyasa da fadin albarkacin, za su goyo masa baya domin tabo wannan batun a tattaunawar da zai yi da gwamnatin Habasha.

GettyImages 163886258 ADDIS ABABA, ETHIOPIA - MARCH 17: German President Joachim Gauck (L) talks with Ethiopian Prime Minister Hailemariam Desalegn before dinner at the Presidential Palace on the first day of his official visit on March 17, 2013 in Addis Ababa, Ethiopia. President Gauck and his partner, German First Lady Daniela Schadt, are in Ethiopia for a four-day state visit. (Photo by Sean Gallup/Getty Images)
Joachim Gauck da Firaminista Hailemariam DesalegnHoto: Getty Images

"Yanzu haka an takaita 'yancin fadin albarkacin baki da na walwalar jama'a da siyasa, ana kuma tsare da 'yan adawa da 'yan jarida da dama masu sukar lamirin gwamnati, roko na shi ne shugaba Gauck ya fito karara da wannan batun a gaban shugabannin Habasha."

Habasha na daya faga cikin kasashe masu muhimmanci dake da hadin kan tattalin ayyukan rasa kasa da tarayyar Jamus. A dangane da matakan ba sani ba sabo da gwamnati a birnin Addis Ababa ke dauka kan al'umarta, ya zame wa gwamnatin Jamus dole ta rage yawan taimakon da take ba wa kasar.

Mawallafa; Ludger Schadomsky / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar