1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara daya da kai harin Boko Haram a Mubi

Thomas Mösch/ USUOctober 21, 2015

A karshen watan Oktoba na shekara ta 2014 ne kungiyar Boko Haram ta kai hari a Mubi, birni na biyu mafi girma a jihar Adamawa, da niyyar mayar da shi babban birnin daularta ta Islama.

https://p.dw.com/p/1GsKi
Hoto: DW/I. Abubakar

Daular da ta yi ikirarin kafawa da yankunan da suka ratsa cikin arewacin makociyar Najeriya wato Kamaru da kuma jihar Borno, amma makonni biyu kadai ta iya yi tana rike da wannan birni. Tosai dai wannan bai hana mazauna Mubin tserewa ba, musamman Kiristoci marasa rinjaye. Yanzu shekara daya ke nan da afkuwar wannan lamari. Daga mutun ya shiga Mubi zai iske wani yanayi ne na hada-hada mai ban mamaki, sai ka ga ana gudanar da lamura kamar dai yadda suke a sauran manyan biranen Najeriya. Sai dai a babban titin birnin za ka ga manyan gine-ginen da 'yan ta'addan suka lalata.

Nigeria Mubi Pfarrer Ndahi in seinem zerstörten Haus
Hoto: DW/A. Kriesch

Fada Shawulu Auta Ndahi, yana shirin sujada ke nan, wasu mata kusan su 50 sun zauna a fararen kujeru. Daga yanayin kwanon, sabon rufi aka yi wa cocin, amma jikin bangon duk bakin hayaki ne. Mai wa'azin na tune da abubuwan da suka faru ranar 29 ga watan Oktoban bara lokacin da kwatsam labarin ya zo cewa Boko Haram ta shiga Mubi, zuwa ya yi ya kwashe 'ya'yansa a makaranta ya zuba a mota, suka ficce daga garin.

Makonni biyu bayan tafiyar tasa, dakarun soji suka anshe Mubi daga hannun kungiyar amma Ndahi, bai amince ya dawo gida ba sai da ya yi watanni uku. Bayan da ya dawo kuma ya tarar Cocinsu ya kone, gidan shi da ke kusa da cocin, shi ma sai bura-buzai kadai ya rage, ba sauran abin da ya mallaka.. to ko yaya ya ji?

"Na yi fushi sosai domin duk abin da na shafe shekaru ina fafutukar nema, cikin mintoci kalilan na rasa su baki daya."

Yadda Fada Ndahi ke ji, haka mutane da dama a Mubi suke ji, domin lokacin da Boko Haram ta kai wadan nan hare-haren kusan babu cocin da ba'a kona ba a cewar shugaban kungiyar kristocin Najeriya CAN a wannan yankin. Mr Anointing Bitrus ya ce a cikin cocuna 150 da ke karkashin wannan kungiya 10 ne kawai ba a kona har kasa ba

Shawulu Auta Ndahi
Shawulu Auta NdahiHoto: DW/A. Kriesch

"Yadda muke ganin wannan al'amari shi ne: wa ya aikata wannan ta'asar, 'ya'yan wane ne su, domin wata sa'a tunanin wadanda suka aikata wannan abu ba karamin daure kai ya ke da shi ba, idan ka kalla daga wani bangaren za ka ga cewa ba Kiristoci ne suka yi ba, shi ya sa muke shakkun addinsu."

Bitrus ya ce yana so Kiristocin su sami tsaro, amma har yanzu ana samun hare-hare a kauyuka. Banda tsaro, fatanshi ma shi ne a yi la'akari da asarar da suka yi, ba ma na dukiya kadai ba, har ma da wanda ya shafi jikinsu, sai da gwamnati a Yola ta ki ta bayar da fiska.

Tafiyar 'yan mintoci kadan sarki Abubakar Ahmadu na karbar baki a fadansa bayan Jumma'a...

Sarkin ya bayyana cewa rayuwa ta daidaita a Mubi, bankunan da ke rufe har yanzun ne kawai ke kawo matsala tunda sai an yi tafiyar awa hudu zuwa Yola kafin a ciro kudi amma dangantakar musulmi da Kirista a ra'ayinsa bata fiskantar wata matsala.

Sarkin Abubakar Ahmadu
Sarkin Abubakar AhmaduHoto: DW/I. Abubakar

"A nan a Mubi mutun bai iya gane wanda ke musulmi da wanda ke kirista, domin mun zama al'umma guda. A gida daya ma kana iya ganin cewa babban dan Kirista ne shi kuma kanin shi ya kasance musulmi. Za su iya yakar junansu ne? Mubi daya ne, bamu da wata matsalar addini tsakanin musulmi da kirista. Ni ne sarkin Mubi, kuma ina kwatanta wa kowa adalci."

A Yola, fadar gwamnati, kwamishinan yada labarai Ahmed Sajoh wanda shi kansa ya fito daga Mubi ya san cewa akwai rashin yarda tsakanin addinan biyu a wasu lokuta, kuma gina yadda a tsakanin al'ummar na da mahimmancin gaske ga gwamnati, shi ya sa suke aiki kafada-da kafada da kungiyoyin addinan biyu shi ya sa bai fahimci korafin kiristocin ba...

"Watakila suna tsammanin za'a basu kudi su sake gina cocunansu ne. Inda za mu iya, da mun yi amma bamu da isasshen kudi, shi ya sa muke neman wasu karin hanyoyin samun kudade."

A cewar ministan dai, wannan rashin kudin ne ma ya sanyasu mayar da sake gina makarantu da sauran ababen more rayuwa a jihar kan gaba kafin saura su biyo baya.