1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron fafutukar 'yancin Afirka

Daniel Pelz
February 19, 2019

Taron da aka yi a birnin Paris na da nufin samarwa nahiyar 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka da karin 'yancin walwala tsakanin bakaken fata a fadin duniya, taron da ya jagoranci samarwa Afirka matsayinta a yau.

https://p.dw.com/p/3Dern
Äthiopien AU in Addis Abeba
Hoto: DW/G. Giorgis

A ranar 19 ga watan Febrairu shekaru 100 da aka gudanar da taron fafutukar hadin kan Afirka na farko a birnin Paris. Taron na da nufin samarwa nahiyar 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, da karin 'yanci da walwala tsakanin bakaken fata a fadin duniya.

A watan Nuwamban shekara ta 1918 Tarayyar Jamus ta yi asara a yakin duniya na daya. Hakan ya sa wajibi aka tattauna yarjejeniyar sulhu. Marubuci kuma masanin tarihi na Amurka Du Bois ya ce zai kasance abun kunya ga bakaken fata sama da miliyan 200 da ke fadin duniya, ace basu da wakili a wannan zauren mashawarta na samar da sauyi a duniya.

Ba Amurken Du Bois na da nasa shiri  na cimma wata manufa da sauran matafiya 'yan uwansa da ke tababa a akai, taron babaken fata daga nahiyar Afirka da Amurka da wasu yankuna na duniya a tsakiyar birnin Paris, tare da neman biyan wasu bukatu da aka gabatarwa masu tattaunawar zaman lafiya.

Farfesan nazarin nahiyar Afirka a jami'ar Kwalambiya da ke birnin New York Mamadou Diouf ya shaidawa DW cewar Du Bois na ganin cewar Afirka na cikin ko wane shiri, bayan yakin duniya na daya:

Blaise Adolphe Diagne
Dan siyasar kasar Senegal Blaise Adolphe Diagne Hoto: Public Domain

"An gudanar da taron a birnin Paris ne saboda wani dalili. An yi taron ne a karkashin tsarin taron zaman lafiya. Manufar shugabannin Afirka na tursasa gudanar da wannan taron shi ne, na ganin cewa nahiyar na da wakilci a lokacin mahawarar. Kuma wajibi ne 'yan Afrikan da kansu su gabatar da wadannan batutuwa, kana bayyanarsu zai nuna irin matsayin da Afirka ta ta ke da shi a zahiri bayan yakin duniya na farko".

Jim kadan bayan yakin duniya na daya dai, a bayyane ta ke cewar daular mulkin mallaka ta Tarayyar Jamus ta doshi karewa. Batun da kuma masanin tarihi Du Bois ya hango tun da wuri, kamar yadda farfessan da ke nazarin tarihin Afirka a jami'ar Humbolt da ke birnin Berlin Andreas Eckert ya nunar:

" Tun da farko Du Bois ya hango cewar 'yan siyasar nahiyar Turai da na Arewacin Amurka basa da muradin baiwa yankunan da suke wa mulkin mallaka 'yan cin kai. Sai dai ya yi kokarin amfani da damar da yake da ita wajen nunar da cewa,  wajibi ne a tattauna akan muhimman batutuwa da suka jibanci inganta rayuwar al'ummomin da ke rayuwa cikin yanayin na mulkin mallaka".

 An sha gwagwarmayar tabbatar da wannan taro da wakilai 57, to amma 16 daga cikinsu daga Amirka suka fito. Sai dai ganawar ba ganawa ce mai sauki da bakaken fata 'yan Afirka ba. Kamar yadda Farfesa Mamadou Diouf ya bayyana:

" Wannan batu ne da ke da muhimmanci da ya dace a yi la'akari da shi, saboda a wancan lokacin lokaci ne da aka fara gwagwarmayar 'yanta Afirka, da wadanda ke da tushe daga nahiyar Afirka a fadin duniya, lamarin da bai yi tasirin kai tsaye ba kan tattaunawar, amma  kuma ya taimaka a gwagwarmayar data biyo baya".

W.E.B. Du Bois US-amerikanischer Bürgerrechtler
Mai fafututika W.E.B. Du BoisHoto: Getty Images/C. M. Battey

Sai dai daga sannan kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, domin Blaise Diagne dan asalin kasar Senegal  ya zama dan majalisar Faransa na farko bakar fata da ya samu shiga gwamnti. Kuma daga nan ne aka shiga gudanar da irin wadannan taruruka tsakanin matasan Afirka a biranen Amurka da kasashen Turai.

Da yawa daga cikin matasan wancan lokaci ne suka jagoranci kasashensu zuwa samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, sannan a cikinsu akwai Jomo Kenyatta na Kenya da Kwame Nkuruma na Ghana. Hasali ma Nkuruma ne ya shirya fitaccen taron bakaken fatar na farko a wata kasar Afirka wanda a ka yi a birnin Accra a shekarar 1958. Sannu a hankali aka samu Kungiyar hada kan kasashen nahiyar Afirka wadda a yau ta zama Tarayyar Afirka.