1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 25 da murkushe boren demokradiyya a China

June 4, 2014

Har yanzu kuwa babu wanda ya isa ambaton dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a kan dalibai da suka yi gangami a dandali Tiananmen da ma sakamakonsa.

https://p.dw.com/p/1CBst
Bildergalerie Tiananmen
Hoto: Jeff Widener/AP

Shekaru 25 bayan da aka yi wa masu gangamin neman sauyi a dandalin 'yanci na Tiananmen da ke birnin Beijing, har yanzu babu wanda ya isa ambaton wannan dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a kan daliban da suka yi gangamin da ma sakamakonsa. Akwai mutanen da ke rayuwa tsawon wannan lokaci, amma ba za su iya magana da kowa a kan ta'assar ba. Kuma ga mafi yawansu ranar 4 ga watan Junin shekarata 1989, rana ce da ba za su taba mantawa ba har iya rayuwarsu.

A kowace rana dubban baki ne ke tururuwa zuwa wannan dandali na Tiananmen tun daga fitowar rana, inda sukan yi bukukuwan rera taken kasar da daga tutoci, tare da daukar hotuna a kusa da mutum-mutumi na Mao da ke da bangaren arewacin dandalin. Sai dai ga Ma Shaofang wannan rana ce ta baklin ciki da juyayi da ba zai taba mantawa a rayuwarsa ba. A rana kamar ta yau shekaru 25 da suka gabata, Ma ya kasance a jerin farko na daliban da ke zanga-zangar, wanda kuma ya ce.

"Muna rera wakokin kasa da kasa, muna ihun cewar banda cin zarafi. Jibge a gabanmu tankunan sojoji ne, da jami'ai dauke da manyan makamai. A bayanmu kuma akwai kimanin mutane dubu 10. Daga nan sojojin suka tunkare mu, mu kuma muka fara yin baya baya."

Rashin yarda da jam'iyyar Kwaminisanci

Bildergalerie Tiananmen
Hoto: Jeff Widener/AP

A yanzu haka dai Ma Shaofang yana harkokin kasuwancinsa ne a yankin kudancin kasar. A shekarar ta 1989 kuwa ya kasance daya daga cikin shugabannin dalibai, lokacin da dalibai wajen dubu 10 suka gudanar da gangamin yaki da cin hanci da neman karin 'yancin fadin albarkacin baki. Daga baya dai Ma ya kasance mutum na 10 da gwamnati ke nema ruwa a jallo. Inda daga bisani ya yi zaman kurkuku na shekaru uku. Ma mai shekaru 50 da haihuwa, yana harkokin kasuwancinsa a garin Shenzhen da ke kudancin China- ba ya da muradin kasancewa a Beijing ko kadan. Ma ya ce yanzu haka ba shi da imani a jam'iyyar kwaminisanci da a baya suka yi mako guda suna yin gangami a kanta.

"A lokacin da muke zanga-zangar neman 'yanci ga jama'a da kasarmu, ba mu san cewar jam'iyyar ba ta tare da al'umma ba, balle mayar da su tamkar abokan gabarta. A yanzu haka wannan jam'iyya ba ta da kima a idona."

Wannan bawan Allah dai, da wuya ya yi tsokaci kan shekarar ta 1989. Ko mene ne dalili? Shi ma dai yana da masaniya, babu wanda zai saurareshi, kasancewar 4 ga watan Yuni haramtacciyar rana ce ta ambato a kafofin yada labaru da kafar sadarwa ta yanar gizo ko kuma Internet.

Sanya ido kan masu sukar lamirin gwamnati

Zhang Xianlang ta kasance tsohuwar shugabar dalibai, kamar Ma. Mai shekaru 76 da haihuwa kuma mai ritaya ta rasa danta mai shekaru 19 wanda aka harba a kai. Ba ta samu nasara tserewa daga China a lokacin ba ko da kuwa tana da niyyar hakan, kuma har yanzu hukumomi na sa ido a kanta, ana tozarta mata, kazalika ba ta da ikon kai ziyara ketaren kasar. Har ila yau kuma idanun hukumomi yana kan duk mutumin da ya cika yawan tambaya, ciki har da iyalan wanda abun ya ritsa da su a wancan gwagwarmayar.

Hunderte Menschen demonstrieren vor Tiananmen-Jahrestag in Hongkong 1.6.2014
Hoto: AFP/Getty Images

Zhang ta ce: "suna take 'yancinmu da kafafunsu. Sun bindige dana shekaru 25 da suka gabata. Suna take hakkokinmu, ba mu da 'yanci. Ko wace shekara idan 4 ga watan Yuni ta kusa, a kan sa mana idanu, wani lokaci mutane biyu ne za su rika bibiyarka, wasu lokuta har idan zan je cefane a kasuwa ko zan tafi asibiti."

A hukumance babu wani juyayi dangane da wannan rana, kazalika kawo wannan lokaci babu takamammen adadin mutanen da suka rasa rayukansu, sai dai uwaye mata na yaran da suka yi wancan gangami na gwagwarmaya 200 sun gabatar da sunan 'ya'yansu, sai dai akwai yiwuwar karin yawan wadanda aka kashe a ranar 4 ga watan Yunin 1989.

Mawallafa: Ruth Kirchner / Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Mohammad Nasiru Awal