1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 56 da fara Bundesliga a Jamus

July 18, 2013

Ranar 28 ga watan Yuli na shekara ta 1962 a birnin Dortmund aka yanke shawarar fara wasannin na Bundesliga. A kakar bana, wasannin kwallon kafa na Lig din Jamus yake cika shekaru 56 da kirkiro shi.

https://p.dw.com/p/19ABq
Hoto: picture-alliance/dpa

Ranar 28 ga watan Yuli na shekara ta 1962, lokacin shawarwari a zauren shawara na Westfalenhalle a Dortmund aka yanke shawarar fara wasannin na Bundesliga. A yau, Lig na Bundesliga ya zama wani kamfani mai zaman kansa dake da jarin Euro miliyoyi dubbai.

Nasarar Bundesliga ta zama al'amarin da ba'a taba samun irinta ba a tarihi. A ko wane mako, wasannin Bundesliga, sukan ja hankalin 'yan kallon da ba'a iya kidaya su zuwa filayen wasanni dabam daban, duk kuwa da sanin cewar sai da aka sha matukar wahala kafin a kai ga kirkiro wasannin na Bundesliga. Bayan zaman shawarwari, ranar 28 ga watan Yuli na shekara ta 1962, haka ta cimma ruwa. Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa, wato DFB, Wolfgang Niersbach ya ce:

"A game da wasan kwallon kafa a Jamus, daukar wannan mataki shi ne mafi muhimmanci da aka taba samu, saboda a taron an yanke kudirin kirkiro wani rukuni na Lig na kasa baki daya. Saboda haka ne wannan kudiri ya zama wani mataki mai muhimmanci a tarihin kwallon kafar Jamus."

Wolfgang Niersbach
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamus Wolfgang NiersbachHoto: picture-alliance/dpa

Gaba daya kungiyoyi 46 ne suka gabatar da takardunsu na neman kasancewa wani bangare na rukunin Lig na daya, wato Bundesliga, inda daga cikinsu akwai kungiyar Hamburg, wadda ta shafe shekaru 55 na wasa a rukunin na Bundesliga, kafin a taba sauke ta zuwa rukuni na biyu. Kungiyoyin da ba'a zabe su a karon farko zuwa Bundesliga ba sun hada da Bayern Munich da Borussia Mönchengladbach, wadanda sai a shekara ta 1965 suka sami nasarar zuwa rukunin na Bundesliga.

Sakamakon kirkiro Bundesliga, 'yan wasa a karon farko, sun sami damar samun kudi daga sana'arsu, ko da shike ba wani kudin kirki ba ne, saboda an kayyade albashin 'yan wasan ya zuwa misalin DM 1200 ne kawai a wata. Tsohon dan wasan Cologne mai suna Hans Schäfer ya ce, "ba na son in nuna cewar 'yan wasan da ke wasanninsu yanzu a Bundesliga suna hakan saboda dimbin kudin da suke samu kawai." To amma 'yan wasan wannan zamani sukan yi mamakin dan abin da 'yan wasan da suke samu a matsasyin albashi.

Dan wasan Bayern Munich Philipp Lahm alal misali, albashin sa a yanzu ya kai Euro dubu 583 ne a kowane wata. A da can, ya zama tilas dan wasa bayan kwallon kafa, ya nemi wani abin yi dabam. Günter Netzer na Mönchengladbach yayi aiki a gidn rawa, yayin da Uwe Seeler na Hamburg ya rika aiki a kamfanin Adidas.

Uwe Seeler ya ce: " Babu wani lokacin da na dogara gaba daya ga wasan kwallon kafa kawai, saboda ba zan iya rayuwa da kwallon kafan ba. Da dan abin da nake samu DM 1200 ko 1500 kafin haraji, ko wani gidan kirki ma ba zan iya samu a nan Hamburg ba."

Kakar Bundesliga ta farko an shige ta ne a shekara ta 1963, inda kungiyar da ta zama zakara a kakar Bundesliga ta farko a Jamus ita ce FC Cologne karkashin jagorancin Wolfgang Overath.

A shekaru na saba'in, Bundesliga ya fuskanci abin kunyarsa na farko, ta hanyar hada baki da biyan 'yan wasa da jami'ai kudi domin cuta da murdiya a wasu wasanni. A sakamakon wannan hanya ta cuta, kungiyoyin Rot-Weiß Oberhausen da Armenia Bielefeld suka kaucewa komawarsu zuwa rukuni na biyu na Lig.

Jupp Heynckes
Burin ko wace kungiyar kwallon kafa a BundesligaHoto: Getty Images

Kakar Bundesliga da aka kare a 2012, ita ce mafi samun nasara tun da aka kirkiro Lig din shekaru 50 da suka wuce. Kungiyoyin na Bundesliga sun sami kudi misalin Euro miliyan dubu daya da dari bakwai da hamsin, inda a duk tsawon kakar, 'yan kallo akalla dubu 45 suka rika shiga filayen wasanni a kowane mako, adadi mai yawa a Turai baki daya. Bundeliga dai yana ci-gaba da bunkasa. Mai koyar da 'yan wasa Otto Rehhagel ya bayyana dalilin hakan:

Ya ce "babu wani abin da ya canza a yanayin wasa a da can da kuma yanzu. Filin wasa har yanzu yana da fadin mita 60 n da tsawon mita 100, babu abin da ya canza. A da can kuma, babu wani dan wasa dake iya gudun mita 100 a tsakanin lokcin da bai kai dakika 10 ba. A yanzu ma haka ne babu wani abin da ya canza."

Sai dai wasan a yanzu yafi na da can sauri, saboda haka yafi ban sha'awa, inji Rehhagel. Wani abu guda kuma da yake tabbas shi ne: har yanzu ba'a hangi lokacin karewar nasarorin da Bundesliga yake samu, ko zai ci gaba da samu ba.

Mawallafa: Thomas Klein / Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal/ Mouhamadou Awal Balarabe